✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mikel Obi zai halarci gasar cin kofin Afirka

A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagles John Obi Mikel ya bayar da tabbacin zai halarci gasar cin kofin Afirka…

A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagles John Obi Mikel ya bayar da tabbacin zai halarci gasar cin kofin Afirka da za a yi a Masar a watan gobe.

Dan kwallon ne da kansa ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a shafin sadarwarsa na Instagram.

John  Mikel Obi ya ce “ina mai shaida muku cewa na yanke shawarar buga wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles wasa a yayin gasar cin kofin Afirka da za a yi a Masar a watan Yunin wannan shekara kuma tuni na sanar da kocin kungiyar Gernot Rohr a game da wannan batu.”

A baya an yi ta rade-radcin Mikel ba zai halarci gasar ba Mikel Obi da hakan ya jefa da yawa daga cikin magoya bayan Super Eagles cikin rudani. Sai dai wannan furuci da dan kwallon ya yi a yanzu ya kawar da wancan shakku.

Mikel Obi yana daga cikin zaratan ’yan kwallon Super Eagles don haka rashinsa ba karamar illa ba ce a kungiyar.