✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Minista Sadiya ta auri Air Marshal Sadique

Sabbin ma'auratan sun dade suna soyayya kafin a daura auren a ranar Juma'a

Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar, ya auri Ministar Jinkai, Agaji da Bunkasa Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar-Farouq.

Majiyoyinmu sun tabbatar mana da cewa an daura auren ne a ranar Juma’a 18 ga Satumba, 2020 a Masallacin Jama’a na Maitama da ke Abuja, da dare.

“Gaskiya ne an daura auren Babban Hafsan Sojin Sama da Ministar Jinkai da Agaji da Bunkasa Rauywa.

“Mutane ’yan kadan ne aka gayyata su halarci daurin auren saboda ma’auratan da makusantansu ba sa so a yayata shi sosai”, a cewar daya daga cikin majiyoyin.

Wata majiyar kuma ta ce sabbin ma’auratan “sun dade suna soyayya kuma daurin auren na ranar Juma’a ya kawo karshen hasashen masu tunanin akwai soyayya a tsakaninta da Shugaba Buhari”.

Idan ba a manta ba a watan Oktoban 2019 an yi ta jita-jitar cewa an daura auren Shugaban Kasa Buhari da Minista Sadiya Umar-Farouq cikin sirri kafin daga baya Fadar Shugaban Kasa ta karyata labarin.