Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Ministan Wasanni ya nemi a yi bincike kan kisan dan kwallo Tiamiyu Kazeem

Ministan Wasanni ya nemi a yi bincike kan kisan dan kwallo Tiamiyu Kazeem

Ministan Matasa da Wasanni, Mista Sunday Dare ya yi tir da kisan gillar da wadansu ’yan sandan sashin yaki da fashi da makamai suka yi wa matashin dan kwallon kafa Tiyamiyu Kazeem da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Remo Stars ta garin Shagamu.

Minisan ya ce irin wadannan kashe-kashe da ake yi wa matasa na daya daga cikin dalilan da suke kara kawo ci baya a kasar nan.

“Kisan wannan matashin dan kwallo na Remo Stars, Tiyamiyu Kazeem abin takaici ne sosai kuma bai kamata ba,” inji Minista Dare.

“A yayin da nake mika sakon ta’aziyyata ga danginsa da kuma Kungiyar Remo da duk sauran masoya wasan kwallo, ina kira ga Rundunar ’Yan sanda ta Kasa ta binciki wannan lamarin ta tabbatar ta hukunta masu hannu a ciki.

Rahotanni sun ce dan wasan na Remo Stars ya hadu da ajalinsa ne yayin da ’yan sandan suka kama shi bisa zargin ya yi kama da ’yan damfarar Intanet da aka fi sani da  Yahoo Boys, wanda daga bisani da suka fuskanci ba ya daya daga cikin wadanda suka zo kamawa sai kawai suka turo shi daga cikin motarsu da take gudu, inda take wata mota da ke biye da su ta take shi. Duk da yake an yi gaggawar daukarsa zuwa asibiti amma likitoci sun tabbatar da cewa rai ya yi halinsa yayin da suka duba shi.