✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministar Lafiya ta Birtaniya ta kamu da cutar Kurona

Ministar Lafiya ta kasar Birtaniya, wacce ’yar Majalisar Dokoki CE daga Jam’iyyar Conserbatibes, Misis Nadine Dorries ta kamu da cutar Kurona. Ita ce ’yar Majalisar…

Ministar Lafiya ta kasar Birtaniya, wacce ’yar Majalisar Dokoki CE daga Jam’iyyar Conserbatibes, Misis Nadine Dorries ta kamu da cutar Kurona. Ita ce ’yar Majalisar Dokokin kasar ta farko da ta kamu da cutar.

Ministar ta sanar cewa a yanzu ta killace kanta a gida, yayin da hukumomi ke ta kokarin gano inda ta kwaso cutar.

Ma’aikatar Lafiya ta Kasar ta ce Misis Dorries ta fara nuna alamun cutar a ranar Alhamis din makon jiya, ranar da ta halarci wani taro cin abinci da Firayi Ministan Birtaniya Boris Johnson ya shirya a fadar gwamnati da ke Titin Downing.

Sai dai Fadar Downing ba ta ce ko an yi wa Firayi Minista Boris Johnson gwajin kwayar cutar ko kuma nan gaba ne za a yi masa gwajin ba.

Kusan mutum 400 ne cutar Kurona ta kama a Birtaniya inda shida suka mutu. Mutumin da cutar ta hallaka a baya-bayan nan a Birtaniya, shi ne wani dattijo mai shekara 80 bayan ya yi fama da cutar.

Sai dai har yanzu ba a iya tantance adadin mutanen da Misis Dorries ta yi mu’amala da su a zauren majalisar da ke Westminster ko kuma a mazabarta, cikin ’yan kwanakin nan ba.

Wata ’yar Majalisar Dokokin Kasar, Rachael Maskell, ta wallafa a Tiwita cewa “An umarce ni da in killace kaina sakamakon haduwa da na yi da Misis Dorries ranar Alhamis din makon jiya,” inji ta.

Misis Dorries ta ce ta damu matuka kan makomar lafiyar mahaifiyarta mai shekara 84 wadda a yanzu haka suke zaune a gida daya.