✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministoci 10 da za su fuskanci kalubale mai yawa

A shekaranjiya Laraba ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da ministocinsa 43, wadanda su ne za su taya shi gudanar da mulkin kasar nan…

A shekaranjiya Laraba ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da ministocinsa 43, wadanda su ne za su taya shi gudanar da mulkin kasar nan a karo na biyu.

Shugaba Buhari wanda aka zabe a karo na biyu a watan Fabrairun bana, ya tura sunayen ministocin ga Majalisar Dattawa ne bayan kusan wata biyu da rantsar da shi a watan Mayu da ya gabata.

Wannan ne karo na farko da aka samu ministoci masu yawa fiye da kowane lokaci a tarihin Najeriya, domin jadawalin da Fadar Shugaban Kasa ta fitar ya nuna cewa shi kansa Shugaba Buhari shi ne cikon minista na 44.

A zagayen mulkinsa na farko, Shugaba Buhari ya yi aiki ne da ministoci 36, kamar yadda dokar kasa ta ce tilas ne kowace jiha a Najeriya ta samu wakilci a Majalisar Ministoci.

A wannan karo, Shugaba Buhari ya fadada majalisar inda bayan ya bai wa kowace jiha gurbi daya, sai ya sake komawa yankuna shida da ake amfani da su wajen kason al’amuran siyasa ya sake dauko wadansu fitattun ’yan siyasa a matsayin ministoci.

A yanzu dai Shugaba Buhari ya rantsar da manyan ministoci 39 da kuma kananan ministoci 15. A cikin ministocin akwai guda 14 da suka yi aiki da shi a zangonsa na farko; sa’annan guda 29 sababbi ne.

Shugaban a wannan karon ya kirkiro sababbin ma’aikatu guda uku, wadanda suka hada da Ma’aikatar Kula da Harkokin ’Yan Sanda da ta Ayyuka Na Musamman da kuma Ma’aikatar Jinkan Al’umma.

Kazalika Shugaba Buhari ya rage girman ma’aikatu  biyu, inda ya cire Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama daga Ma’aikatar Sufuri; haka ya cire Ma’aikatar Wutar Lantarki daga Babbar Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje.

Yadda Shugaba Buhari ya yi kason ma’aikatu:

Dokta Ikechukwu Ogah (Abiya), Minista a Ma’aikatar Tama da Karafa, Mohammed Musa Bello (Adamawa), Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Al’amuran Neja-Delta, Chris Ngige (Anambra), Ministan Kwadago, Sharon Ikeazor (Anambra), Minista a Ma’aikatar Muhalli, Adamu Adamu (Bauchi), Ministan Ilimi, Ambassada Maryam Katagun (Bauchi), Ministar Ciniki da Zuba Jari da Timipre Sylba (Bayalsa), Minista a Ma’aikatar Man Fetur.                                                                                                                                                            Saura sun hada da George Akume (Benuwai), Ministan Ayyuka Na Musamman, Mustapha Baba Shehuri (Barno), Minista a Ma’aikatar Gona  da Raya Karkara, Goddy  Jedy Agba (Kuros Riba, Minista a Ma’aikatar Makamashi, Festus Keyamo (Delta), Minista a Ma’aikatar Al’amuran Neja-Delta, Ogbonnaya Onu (Ebonyi), Ministan Kimiyya da Fasaha, Osagie Ehanire (Edo), Ministan Lafiya).

Akwai kuma Clement Ike  (Edo), Ministan a Ma’aikatar Kudi da Kasafi da Tsare-Tsare, Richard Adeniyi Adebayo (Ekiti), Masana’antu da Kasuwanci, Geoffrey Onyeama (Enugu), Ministan Harkokin Kasashen Waje); Ali Isa Pantami (Gombe), Ministan Sadarwa, Emeka Nwajiuba (Imo), Minista a Ma’aikatar Ilimi), Suleiman Adamu (Jigawa), Ministan Albarkatun Ruwa, Zainab Ahmed (Kaduna), Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare), Muhammad Mahmood (Kaduna), Ministan Muhalli.

Sai Sabo Nanono (Kano), Ministan Gona da Raya da Karkara, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (Kano), Ministan Tsaro, Hadi Sirika (Katsina), Ministan Sufurin Jiragen Sama, Abubakar Malami (Kebbi), Ministan Shari’a, Ramatu Tijjani  (Kogi), Minista a Ma’aikatar Babban Birnin Tarayya, Lai Mohammed (Kwara), Ministan Labarai da Al’adu), Gbemisola  Saraki (Kwara), Ministar a Ma’aikatar Sufuri); Babatunde Fashola (Legas), Ministan Ayyuka da Gidaje), Adeleke Mamora (Legas), Minista a Ma’aikatar Lafiya), Mohammed H. Abdullahi (Nasarawa), Minista a Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da Zubair Dada (Neja), Minista a Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje.

Sauran su ne Olamilekan Adegbite (Ogun), Ministan Tama da Karafa, Tayo Alasoadura  (Ondo), Minista a Ma’aikatar Kwadago da Ingancin Aiki, Rauf Aregbesola (Osun), Harkokin Cikin Gida, Sunday Dare (Oyo), Wasanni, Paulen Talen (Filato), Ministar Al’amuran Mata, Rotimi Amaechi (Ribas), Ministan Sufuri, Maigarai Dingyadi (Sakkwato), Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Sale  Mamman (Taraba), Makamashi; Abubakar D. Aliyu (Yobe), Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje) da kuma Sadiya Umar Faruk (Zamfara), Ministar Ayyukan Jinkan Jama’a.

Kason ya nuna cewa jihohin Bauchi da Kaduna da Kano da Katsina sun samu manyan ministoci bibbiyu; abin da masu fashin baki ke ganin kamar tukwici ne na musamman kan irin yadda jama’ar jihohi suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka zabi Shugaba Buhari a karo na daya da na biyu. Sai dai jihohin Borno da Yobe, wadanda suka kasance tare da Shugaba Buhari tun fitowarsa siyasa a wannan karo kananan ministoci aka ba su.

A lokacin da yake rantsar da su a fadarsa, Shugaba Buhari ya ce ya fadada majalisar ministocin ce domin a samu ci gaba cikin gaggawa. “Ina farin cikin shaida muku cewa mun fadada ma’aikatu ne domin a samar wa al’ummar Najeriya abubuwan more rayuwa,” inji shi.

Ministocin da za su fuskanci babban kalubale

Duk da cewa kowace ma’aikata tana da muhimmanci, binciken Aminiya ya gano cewa akwai wasu ma’aikatu goma da ministocinsu za su fuskanci kalubale mai yawa.

Ministan Tsaro:

Hakika akwai jan aiki a gaban Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ganin yadda Najeriya ke fama da matsalolin tsaro; kama daga ayyukan ta’addanci na ’yan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas wadanda ko a wannan mako sun kwace garin Gubio, zuwa rikicin manoma da makiyaya, musamman a Arewa ta Yamma da Arewa ta Tsakiya da matsalolin garkuwa da mutane da suka addabi jama’a; ga kuma matsalolin yankin Zamfara da tsageru a yankin Ibo da na Neja-Delta.

Janar Magaji ya gaji tsohon Mininstan Tsaro Janar Mansur Dan-Ali, wanda Buhari ya dauko daga Jihar Zamfara a 2015.

Janar Magashi, wanda haifaffen Jihar Kano ne, gogaggen sojan Najeriya ne kuma ya yi Gwamna a Jihar Sakkwato daga 1990 zuwa 1992 lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya).

Masu fashin baki suna ganin Shugaba Buhari ya ba shi wannan mukami ne saboda cancanta, a matsayinsa na tsohon soja kuma kwararren lauya, wanda ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Kuma ya taba zama Babban Kwamandan Tsaron Shugaban Kasa (Guards Brigade).

Tsaro dai shi ne na farko a jadawalin abubuwan da Shugaba Buhari ya yi alkawarin samarwa.

Ministan Makamashi:

Akwai babban aiki a gaban Injiniya Saleh Mamman, dan asalin Jihar Taraba, wanda Shugaba Buhari ya karbi hidimar Ma’aikatar Makamashi daga hannun tsohon Gwamnan Jihar Legas, Babatunde Fashola ya mika masa.

Samar da wutar lantarki wani babban al’amari ne da ya gagari shugabannin kasar nan da dama tun samun mulkin kai a 1960.

A farkon mulkinsa, Shugaba Buhari ya yi alkawarin warware matsalolin wutar lantarki, wadanda masana suke ganin in aka samu maslaha za a samu ci gaban tattalin arziki domin masana’antu za su bunkasa kuma a samu ayyukan yi ga dimbin matasa.

Haka masu fashin baki na ganin Shugaba Buhari ya nada Saleh Mamman ne a kujerar, domin ya tabbatar da cewa babban dam din Mambila wanda zai samar da wutar lantarki ya tabbata.

Mamman wanda aka haife shi a ranar 2 ga Janairu, 1958, yana da Babbar Diploma (HND) a fannin Lantarki daga Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna kuma yana da babban digiri a fannin kasuwanci daga Jami’ar Bayero, Kano.

Ya yi aikin koyarwa a Technical School Mubi, Jihar Adamawa, daga nan ya koma aiki a jiharsa ta haihuwa a 1992. Ya dauki dogon lokaci yana aiki har ya kai matsayin Daraktan Ayyuka a Ma’aikatar Ayyuka kafin ya yi ritaya a 2002.  Daga nan ne ya zama dan kasuwa kuma gogaggen dan siyasa.

 Ministar Ma’aikatar Jinkan Jama’a

Hajiya Sadiya Umar Faruk, Ministar sabuwar Ma’aikatar Jinkan Jama’a za ta sha fama. A yanzu dai Najeriya tana fama da miliyoyin mutane da suka rasa muhallansu saboda masifu daban-daban.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa a Arewa maso Gabas akwai mutane sama da miliyan biyu da suka yi gudun hijira daga kauyukansu suna zama a sansanonin ’yan gudun hijira; kuma mutane sama da miliyan talatin suna neman agaji.

Jihohin Barno, Yobe, Adamawa, Bauchi, Filato, Benuwai, Kogi, Zamfara, Kaduna da sauransu, duk suna fama da matsalolin ’yan gudun hijira. Sai dai kuma ana ganin Hajiya Sadiya gogaggiyar ma’aikaciya ce a wannan fanni, ganin cewa ta rike mukamin Babbar Kwamishina a Hukumar Kula da ’Yan gudun hijira da bakin haure. Mai shekara 44, Sadiya ’yar asalin Jihar Zamfara ce.

Ministan Ayyuka:

Kwararren Lauya kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Babatunde Fashola ya yi rawar gani a karon farko lokacin da Shugaba Buhari ya hada masa ma’aikatu uku manya.

Masu fashin baki suna ganin har yanzu akwai ayyuka da dama a gabansa, ganin cewa hanyoyin Najeriya da dama ba su da kyau. Haka miliyoyin mutane ba su da muhalli, don haka ana ganin yanzu da aka karbe Ma’aikatar Makamashi daga hannunsa, Fashola zai mai da hankali wajen gyara hanyoyi da gina sababbi da kuma samar da gidaje.

Ministan Kwadago

Chris Ngige, kwararren likita, shi ne Shugaba Buhari ya ce ya ci gaba da kula da ma’aikata da samar da aikin yi. Babban kalubalen da ke gabansa shi ne biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 30. Har yanzu dai ba a cimma matsaya a kai ba, saboda biyan kudin ya faskara, duk da cewa Majalisar Tarayya ta kafa doka kuma Shugaba Buhari ya rattaba mata hannu. Ana ganin in har ba a samu nasarar biyan kudin ba, to ma’aikata za su shiga yajin aiki.

Ministan Lafiya

Shi ma Ministan Lafiya, Osagie Ehanire akwai jan aiki a gabansa, ganin yadda sha’anin kiwon lafiya ke tabarbarewa a kullum. A yanzu dai akwai asibitocin Gwamnatin Tarayya da dama da ba su iya bayar da cikakkiyar kula ga marasa lafiya; dalilin da ya sa likitoci ke guduwa kasashen waje, su kuma masu hannu da shuni suke tsallakawa waje domin neman lafiya.

Ministan Ilimi

Kwararren Akanta kuma gogaggen dan jarida, Malam Adamu Adamu akwai aiki a gabansa, ganin yadda malaman jami’o’i ke barazanar tafiya yajin aiki. Haka kuma a matsalolin kwararrun malamai, ga kuma yadda ake yaye gurbatattun dalibai a makarantu.

Ministan Ma’aikatar Gona

Shugaba Buhari ya dauki aikin noma da muhimmanci. Kan haka ne ya hana shigo da shinkafa da wasu nau’o’in abinci. Akwai aiki a gaban Alhaji Sabo Nanono domin daidaita rikicin da ke tskanin manoma da makiyaya, samar da rugage domin makiyaya da kuma tallafi ga manoma domin su daina yin asara.

Ana zargin tsohon Ministan Gona, Audu Ogbe da cewa bai tabuka abin kirki ba, in ban da surutai, dalilin da ya sa rikici tsakanin manoma da makiyaya ya-ki-ci-ya-ki cinyewa.

Miliyoyin ’yan Najeria sun karbi aikin noma gadan-gadan sai dai kuma akwai matsaloli da ke gallabarsu. A bana manoma da dama sun yi asara saboda farashin abubuwan da suka noma ya fadi kasa.

Ministan Birnin Tarayya

Yawan jama’a a Babban Birnin Tarayya kullum karuwa yake kuma abubuwan more rayuwa suna kasa. Akwai jan aiki a gaban Malam Muhammad Bello, domin sha’anin tsaro yana kara tabarbarewa.

Ministan Watsa labarai

Tuni dai ’yan adawa sun canja wa Alhaji Lai Mohammed suna, saboda suna zarginsa da yawan shata karya wajen kare Gwamnatin Shugaba Buhari.

A baya yakan yi bayanin cewa gwamnati ta kasa tabuka abin kirki ne domin tsohuwar Gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi ta’adi, kuma farashin man fetur ya fadi. To yanzu farashin man fetur ya yi sama, don haka zai yi wahala ’yan Najeriya su ba da uzuri idan har gwamnatin ta gaza.

Shi ma Shugaba Buhari ya ce wannan karon ya dauki tsawon lokaci ne kafin ya zabo ministocinsa, domin yana so ya yi aiki ne da mutanen da ya sani, ba kamar abin da ya faru a baya ba.

Don haka nan da watanni masu zuwa, ’yan Najeriya za su fara bayanin gamsuwa ko akasin haka daga take-taken ministocin.