✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministocin Buhari 2 sun bukaci sarkin Kano ya tsawatarwa masu zanga-zanga

Ministan Tsaro, Bashir Magashi da takwaransa na Noma da Albarkatun Kasa Sabo Nanono, sun bukaci sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero da ya shiga tsakani…

Ministan Tsaro, Bashir Magashi da takwaransa na Noma da Albarkatun Kasa Sabo Nanono, sun bukaci sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero da ya shiga tsakani domin kawo karshen zanga-zangar da matasa ke yi a fadin Jihar.

Ministocin biyun ‘yan asalin jihar Kano, sun yi kiran ne a lokacin da suka kai ziyara fadar sarkin a ranar Litinin.

A cewarsu, sun kai ziyarar ne saboda umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na kowane minista ya koma jiharsa ya gana da da jama’a domin lalubo bakin zaren.

Ziyarar a cewarsu ta zo daidai da muradin da gwamnatin jihar na wanzar da zaman lafiya a fadin jihar.

Da ya ke jawabi a fadar, ministan tsaro, Bashir Magashi ya ce ya zama wajibi a kansa a matsayinsa na jami’in samar da tsaro, ya tabbatar da an samu zaman lafiya a yankinsa.

Ministocin sun kuma bayyana irin tasirin da masu rike da sarautun gargajiya ke da shi wurin samar da zaman lafiya, tare da bukatar matasa da su zauna lafiya domin amfana da irin shirye-shiryen bunkasa rayuwar matasa da gwamnati ta ke bijirowa da su.

A nasa jawabin, sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa shugaba Muhammadu Buhari bisa turo ministocinsa jihar don ganawa da jama’a a kokarin da gwamnati ta ke yi na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Sarkin ya bayyana matasa a matsayin kashin bayan ci gaban kowace al’umma, a saboda haka ne ma ya nemi hadin kan su wajen samar da zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

Daga nan sai ya ba da tabbacin samun cikakken hadin kai da goyan bayan masarautarsa wacce ya ce kofarta za ta kasance a bude a kowanne lokaci wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.