Search
Subscribe
Ministocin da Buhari ya gabatarwa majalisa ya yi daidai -Musa Buba

Ministocin da Buhari ya gabatarwa majalisa ya yi daidai -Musa Buba

Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna Magaji Musa Buba ya bayyana cewa sunayen Ministocin  da shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya gabatarwa majalisa domin neman amincewa, ya yi dai dai. Musa Magaji Buba, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya.

Ya ce, gaskiya mun yi wa Allah godiya kan wadannan sunayen ministoci da shugaban kasa ya gabatarwa majalisa, domin wadannan sunaye ya kunshi mata da matasa da dattawa. Sannan kuma an kawo sababbi da tsofaffin Ministocin da suka gabata.

Musa, ya ce wannan ya nuna cewa shugaba Buhari  ya yi taka tsantsan kuma ya yi tankade da rairaya a wadannan Ministoci da ya zabo.

Ya yi kira ga wadannan Ministoci su taimakawa shugaban  kasa, wajen ganin an ciyar da Najeriya gaba, ta hanyar gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata.

‘’Al’ummar Najeriya yanzu sun zuba ido da fatan ganin abubuwa zasu gyaru a kasar nan, ta hanyar gudunmawar da wadannan Ministoci zasu bayar’’.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin