✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministocin da Buhari ya zabo kwararru ne – Danladi Pasali

Shugaban Kungiyar Yakin Zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari (BCO), ta Kasa, Alhaji Danladi Garba Pasali ya ce ministocin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zabo…

Shugaban Kungiyar Yakin Zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari (BCO), ta Kasa, Alhaji Danladi Garba Pasali ya ce ministocin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zabo a wannan karo kuma ya rantsar a makon jiya kwararru ne a dukkan ma’aikatun da aka tura su. Alhaji Danladi Pasali ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos, fadar Jihar Filato.

Ya ce idan aka duba wadannan ministoci da Shugaba Buhari ya zabo, kuma ya rantsar za a ga sun cancanta domin kwararru ne   a dukkan ma’aikatun da aka tura kowane minista kuma sun yi wa Jam’iyyar APC aiki.

Ya ce da yardar Allah ministocin za su taimaka wa Shugaban Kasa Buhari, wajen dada kawo ci gaba a Najeriya.

Don haka ya yi kira ga ministocin su tsaya su yi aiki tsakani da Allah, kuma su yi koyi da halayen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wajen gudanar da ayyukansu.

Alhaji Danladi Pasali ya yi bayanin cewa idan aka lura  alkawuran  da Shugaba Buhari  ya yi, na inganta tsaro da  bunkasa aikin gona da inganta tattalin arzikin Najeriya, an samu nasara.

Ya ce gwamnatin Buhari ta karbi kasar nan ne kullum ana saka bama-bamai a masallatai da coci-coci, harkokin kasuwanci sun tsaya, kuma babu wasu ayyuka na ci gaba.

“Yanzu tsaro ya inganta a kasar nan, babu maganar tashin bama-bamai a wuraren ibada da kasuwanni da tashoshin mota. Yanzu harkokin noma sun bunkasa, idan ka shiga kauyuka za ka ga yadda mutane suka rungumi aikin noma. Yanzu an samu wasu wurare da jiragen kasa suke ta gudanar da harkokin zirga-zirga a kasar nan,’’ inji shi.

Ya ce da yardar Allah za a kara samun ci gaba a wannan karo na  mulkin Shugaban Kasa Buhari, don haka ya yi kira ga al’ummar Najeriya su ci gaba da yi wa wannan gwamnati addu’a don ta kai ga nasara.