✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Minti 30 da haihuwa ta rubuta jarabawa a gadon asibiti

Wata mata ’yar kasar Habasha mai suna Almaz Derese, ta rubuta jarabawa bayan minti 30 da haihuwarta a gadon asibitin. Almaz Derese, mai kimanin shekara…

Wata mata ’yar kasar Habasha mai suna Almaz Derese, ta rubuta jarabawa bayan minti 30 da haihuwarta a gadon asibitin.

Almaz Derese, mai kimanin shekara 21, haifaffiyar garin Metu da ke Yammacin kasar Ethiopia, ta yi fatan rubuta jarrabawar makarantar Sakandaren da take yi kafin ta haihu amma hukumar makarantar ta dage lokacin yin jarabawar saboda azumin watan Ramadan.

Ta fara nakudar haihuwar ne, a ranar Litinin da ta gabata lokaci kadan kafin fara rubuta jarrabawar.

Misis Almaz, ta ce nazarin karatun jarrabawar da zata rubuta bai zaman mata wata matsala ba duk da yanayin juna biyu da ta take dauke da shi, saboda ba taso ta kai wata shekara mai zuwa kafin ta kammala karatun makarantar.

Almaz, ta rubuta jarabawar Inglishi da ta harshen Amharic da kuma ta lissafi a asibitin ranar Litinin kuma za ta rubuta sauran jarabawar a cibiyar jarabawar kwanaki biyu masu zuwa.

Misis Almaz ta bayyanawa wakilin BBC Afaan Oromoo, cewa “Saboda zumudin in rubuta jarabawa, don haka ban yi nakudar haihuwa mai tsanani ba.”

Mai gidan Almaz, Tadese Tulu, ya ce sai da suka sasanta da hukumar makarantar kafin su amince Almaz ta rubuta jarabawar a asibitin da ta haihu.

A kasar Habasha, an baiwa ’yan mata damar dakatar da karatun Sakanadare bayan wani lokaci su dawo su ci gaba da karatun su daga inda suka tsaya.

A yanzu haka dai Misis Almaz, za ta je ta yi karatun share fagen shiga jami’a na shekara biyu.

Ta ce, ta gamsu da yadda ta rubuta jarabawarta, da kuma yadda ta ce yaronta na cikin koshin lafiya.