✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Misirawa na zargin Amurka da haddasa musu rikici a kasa

Kalaman jami’in difulomasiyyar Amurka suka tunzura mutane suka kara yin zanga-zanga, ind aya bayyana cewa, “wannan dma ta biyu ce” ga Misirawa wajen kokarin kafa…

Magoya bayan Shugaba Mursi sun tada kayar bayaKalaman jami’in difulomasiyyar Amurka suka tunzura mutane suka kara yin zanga-zanga, ind aya bayyana cewa, “wannan dma ta biyu ce” ga Misirawa wajen kokarin kafa dimokuradiyya, banyan an kawar da zababben shugaban kasa. Kuma daukacin magoya bayan Mursi da ’yan adawa, suna zargin Amurka da kulla musu makirci. Don haka jm’iyyun siyasa suka ki amsa gayyatar Burns da ta Catherine Ashton ta Tarayyar Turai
Dubban magoya bayan Mursi sun tare hanyoyi a manyan biranen Masar a lokcin da Jami’in difulomasiyyar Amurkar, mataimakin Sakataren Harkokin Amurka, William burns ya kai ziyara Alkahira, al’amarin da ya haifar da rikici, inda dubban amgoya bayan habararren shugaba, Muhammad Mursi suka tare hanyoyin kasar, wadanda suka hada da biranen Iskandariyya dad a Alkahira. Su kuwa ’yan sand asuka yi ta yi musu rowan barkonon tsohuwa.
An yi mummunan tashin hankali a dandalin Ramses da ke tsakiyar alkahira, inda ’yan sanda suka fafata da magoya bayan Mursi, inda aka yi asarar rayukan mutane bakwai, kmaar yadda Kamfanin duillancin Labarai na kasar MENA ya ruwaito.
Gwamnatin rikon kwarya ta Masar ta fara aiki, inda za tya fuskanci dimbin kalubale, wadanda suka hada da matsalar tsaro, a daidai lokacin da kungiyar ’yan uwa Musulmi na jam’iyyar hambararren shugababn kasa Muhammad Mursi ke shirin sake lalen zanga-zanga.
Manufar shugabannin gwamnatin rikon, ta hada da ganawa da Shugabar sashen kula da harkokin kasashen waje ta kungiyar Tarayyar Turai, Catherine Ashton, wadda ta ziyarci Alkahira, don yin matsin lamba ga gwamnatin kasar ta dawo kan turbar dimokuradiyya.
kungiyar Ikwan da Jam’iyyar Al-Nur sun ki yarda su shiga gwamantin riko, inda suka yi hadin gwiwa wajen jajircewa da zanga-zangar gioyon bayan shugaba Mursi.
Misis Ashton za ta gana Shugaba Adli Mansour da Firayiminista Hazem Beblawi, Ministan Harkokin Waje, Nabil Fahmy da shugaban sojoji Abdel Fattah al-Sisi, wanda ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da shugaba Muirsi a ranar 3 ga watan Yulin bana.
Shugaba Obma na Amurka da Angela Merkei ta Jamus, duk sun yi kira kan a saki hambararren Shugaban Masar, Muhammad Mursi. Shi kuwa takwaransu na Turkiyya, Erdogan Tayyep, ya ce Mursi ne shugaban Masar da ya amince da shi; al’ummar Turkiyya sun yi zanga-zangar nuna goyon baya ga Muhammad Mursi.