✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miyar kabeji da nama

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake miyar kabeji mai nama. Wannan irin…

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake miyar kabeji mai nama. Wannan irin miya tana kara lafiya a jiki sannan tana da dadi idan aka hada ta da farar shinkafa ko da dafaffiyar doya da kuma farar taliya da sauransu. Yana da kyau uwargida ta koyi yadda za ta rika canza dandanon miyarta a koda yaushe. Samun canji a dandanon girki na da alaka da irin kalar magi da kuma kayan kanshin da ake sa wa a lokacin girkin.

Abubuwan da za a bukata

• Kabeji

• Nama

• Man gyada

• Attarugu

• Albasa

• Tumatir

• Magi

• Kori

• Tafarnuwa

Hadi:

Da farko za a samu kabeji sannan a yayyanka  manya-manya sannan a wanke da ruwan gishiri domin kashe kowace irin kwayar cuta da ke ciki sannan a yayyanka albasa da tumatir kwaya biyu kacal sannan a jajjaga attarugu da tafarnuwa.

Daga nan sai  wanke nama sannan a silala da albasa da gishiri kadan bayan ta yi laushi, sai a yayyanka kanana sannan a soya sama-sama. Bayan haka, a dora tukunya a wuta, a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da tumatir da kuma jajjagen attarugu da tafarnuwa a soya. Sannan a dauko naman a zuba ba tare da romon ba. A zuba magi da kori a gauraya a jira su tafasa sau daya sannan a zuba kabejin a gauraya a dan rufe. Bayan mintuna biyu, sai a sake budewa a gauraya sannan a rufe na tsawon mintuna uku sannan a sauke.

A dora a kan shinkafa dafa-duka zazzafa ko kuma farar shinkafa da makamancinsu. A ci dadi lafiya!