✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miyar karkashi da kubewa

  Assalamu alaikum Uwargida. Yaya iyali tare da fatan ana lafiya? A yau na kawo muku yadda ake miyar karkashi da kubewa danya. Wannan miyar…

 

Assalamu alaikum Uwargida. Yaya iyali tare da fatan ana lafiya? A yau na kawo muku yadda ake miyar karkashi da kubewa danya. Wannan miyar dai ba ta cika son yawan kayan hadi ba sannan kowace mace da yadda take yin miyar karkashi. Wata karkashin zalla kawai take girkawa. Amma idan har ana son a ci miyar ta yi dadi sosai kyanta a hada ta da kubewa danya domin jin ainihin gardin miyar da dadinta. Don haka na kawo muku yadda ake wannan miyar karkashi hade da kubewa danya domin sanya kunnen maigida motsi. A ci dadi lafiya.

 

Abubuwan da za a bukata

  • Ganyen karkashi
  • Kubewa danya
  • Tokar miya ko kanwa
  • Attarugu
  • Bandar kifi
  • Nama
  • Albasa
  • Danyar tafarnuwa
  • Garin citta
  • Magi

 

Hadi

A karkade ganyen karkashin tsaf sannan a yayyanka shi kanana sosai. A samu kubewa danya a yayyanka ta sannan a saka a turmi a daka ta yi laushi sosai. In kuma da kanwa za a yi  miyar sai a daka tare da kanwar kadan. Sannan a kwashe a ajiye a gefe. A daka attarugu da tafarnuwa a kwashe. A wanke bandar kifi da ruwan dumi a cire kwayoyin sannan a yayyanka albasa kanana. A dora ruwa a tukunya sannan a silala nama har sai ya yi laushi. Sai a kara ruwa kadan a kan romon naman sannan a zuba yankakkiyar albasar da jajjagen attarugu da garin citta da bandar kifi har sai sun tafasa sannan a dauko kubewar da aka daka a zuba a rika gaurayawa har ta fara nuna sannan a dauki karkashin a zuba a dauki maburgi a burga sannan a ci gaba da juyawa. Idan har ba a sanya kanwa a miyar ba, a wannan lokacin ya kamata a sanya tokar miyar sannan a jika magi ya narke sai a ci gaba da gaurayawa har sai dandanon ya fito sannan a sauke. Za a iya cin wannan miya da tuwon semo ko masara.