Da Dumi Dumi

Miyar shuwaka

Assalamu alaikum Uwargida! barkanmu da sake saduwa  a cikin wannan fili namu mai albarka na girke-girke. Kamar kullum ba zan fasa bada shawara a kan cewa miya ita ce sirrin dadin tuwo ba. Idan har mace ta iya sarrafa nau’o’in miya, lallai kakarta ta yanke saka. Domin maigida ko tafiya zai yi sai ya yi marmarin yin wannan tafiyar da ita. Don haka ne a yau na kawo muku yadda ake miyar shuwaka, tare da fatar za a gwada irin wannan girki don kwarewa a fanin girke-girke.

Abubuwan da za a bukata

  • Ganyen Shuwaka
  • Manja
  • Naman shanu
  • Kayan ciki
  • Bandar kifi
  • Karfasa danya
  • Magi
  • Kori
  • Kifin ‘cryfish’
  • Attarugu

Hadi

A cire fatar danyen kifi karfasa sannan a dora a wuta hade da magi da ruwa sannan a dafa har sai ya yi laushi sosai sannan a sauke. A cire kashin cikin kifin gaba daya , sannan a zuba a turmi a daka shi har sai ya yi laushi sannan a kwashe a ajiye a gefe.

A wanke naman shanu da kayan ciki  a dora a kan wuta da gishiri kadan. Sannan a wanke bandar kifi  a cikin ruwan zafi a cire kayar kifin.

ADVERTISEMENT

Bayan nama da kayan cikin sun nuna sannan a zuba su a cikin tukunya tare da bandar kifin da kifin ‘cryfish’ da kuma dakakkiyar karfasar. Sannan a dauko wankakkiyar shuwaka a wuta da jajjagen attarugu da kori.

Sannan a gauraya su a zuba magi da manja. Idan ganyen shuwakar ya nuna sai a sake gauraya ta a sauke.

Za a iya hada wannan  miya a ci da kowane irin tuwo. A ci dadi lafiya!

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya