✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Monguno bai halarci ganawar Buhari da Manyan Jami’an Tsaro ba

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro (NSA) Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), bai halarci ganawar sirrin da Shugaba Buhari, ya yi da manyan jami’an…

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro (NSA) Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), bai halarci ganawar sirrin da Shugaba Buhari, ya yi da manyan jami’an tsaron kasa ba da aka yi ranar Litinin a fadar shugaban kasa.

Wadanda suka halarci ganawar sun hada da: Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Gabriel Olonisakin da hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai da hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas da hafsan sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar da kuma Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu.

Rahotanni na bayyana cewa,  ganawar ta sirri da aka yi nada alaka da kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta.

A makon jiya ne Janar Monguno, ya tayar da kura a fadar Shugaban Kasa, bayan da ya zargi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar Alhaji Abba Kyari, da yi masa katsalanda a aiki, inda yake tsoma baki a harkokin tsaro ba tare da sanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba.

Janar Monguno, ya yi wannan zargi ne a wata wasika da ya rubuta wadda kuma kafar yada labarai ta Premium Times ta bankado kuma ta wallafa.

A wasikar Janar Monguno, ya ba manyan Hafsoshin sojin kasar nan umarni da su daina bin umarnin da Abba Kyari, ke ba su.