Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Moses Simon ya bude cibiyar horar da matasa kwallo a Kaduna

Moses Simon
Moses Simon

A ranar Asabar da ta gabata ce dan kwallon gaba na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, Moses Simon ya bude wata cibiyar horar da matasa kwallo (Football Academy) a Kaduna.

Simon wanda yake buga wasa a kulob din Lebante na kasar Sifen ya bude cibiyar ce a Hayin Banki da ke garin Kaduna.

ADVERTISEMENT

A yayin kaddamar da cibiyar, an gayyaci tsofaffin ’yan kwallon kafa da masu horarwa da masu ruwa-da-tsaki a harkar kwallo da ’yan siyasa da sauransu.

“Na bude wannan cibiya ce a unguwar da na taso, kuma na san akwai dimbin matasa da suke da kokari a fagen kwallon kafa.  Na yi haka ne don in ba da gudunmawata a unguwar da na taso (Hayin Banki) a matsayina na wanda yake cin gajiyar kwallon kafa,” inji shi.

ADVERTISEMENT

“Ina godiya ga Gwamnatin Jihar Kaduna da Kwalejin Horar da Sojoji ta Kaduna (NDA) da sauran wadanda suka taimaka wajen ganin na samu nasarar bude wannan cibiya,” inji Simon Moses a zantawarsa da Aminiya.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin kaddamar da cibiyar akwai dan kwallon Super Eagles , Francis Benjamin da kanensa Felid Benjamin da Timothy Nansel Simon da Godwin da kuma Joshua Obaje inda suka yi wasan sada zumunta a tsakanin kulob hudu da aka gayyato don burge ’yan kallo.

Sannan a tsofaffin ’yan wasan Eagles da suka halarci bikin akwai Tijjani Babangida da Imama Amapakabo da sauransu.

Cibiyar za ta rika horar da matasa kwallo ne idan sun girma sai a sayar da su ga kulob din da ke bukatarsu a ciki da wajen Najeriya.