✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Motocin kwashe shara uku ne kacal a Jigawa

Karancin ma’aikata da kayan aikin tsaftace muhalli sun addabi Dutse babban birnin jihar Jigawa da sauran manyan biranen da ke fadin jihar. A wani abu…

Karancin ma’aikata da kayan aikin tsaftace muhalli sun addabi Dutse babban birnin jihar Jigawa da sauran manyan biranen da ke fadin jihar.

A wani abu mai kama da almara, Hukumar lura da tsaftar mahalli ta jihar (JISEPA) ta ce motocin kwashe shara uku kacal ne a fadin jihar mai yawan al’umma fiye da miliyan hudu.

Yanzu haka hukumar tsaftace garin Dutse (DCDA) ba ta iya gudanar da aikinta yadda ya kamata, inji Manajan Daraktan hukumar lura da tsaftace muhallin jihar (JISEPA), Malam Umar Ahmed Babura.

A hirarsa da wakilin Aminiya ranar Talata a Dutse, Malam Umar ya bukaci gwamnatin jihar ta samar da karin motocin kwasar bola guda goma, sannan ta sanya baki kowaccce daga cikin kananan hukumomin jihar 27 ta sayi motar kwasar shara akallah guda daya.

Jami’in ya yi kira ga jama’ar jihar su ba wa hukumar hadin kai wajen lura da tsaftar mahallinsu ta hanyar kwashe sharar da kauce wa toshe magudanan ruwa da kuma kulawa da ingancin mahallinsu.

Yin haka a cewarsa, zai rage yaduwar cututtuka a tsakanin jama’a.

Da yake magana game da lalacewar muhalli a garin, jami’in ya dora laifin hakan a kan ‘yan kasuwa da ke zuba shara a gaban kantunans da masu zubawa a wuraren da basu dace ba.

A cewarsa, “matsalar Jihar Jigawa, musamman nan babban Birnin jihar ya tarune a Kasuwar ‘Yan Tifa. A nan ne ‘yan kasuwa ke zubar da shara, ba sa share gaban shagunansu kuma hukumar DCDA ba ta kwashe sharar.

“Shi [ya sa] idan shara da ledoji suka yi yawa a lokacin ruwan sama, suke tafiya su toshe dukkan magudanun ruwanmu.

Shi ya sa shara take mamaye kan titi,  wani lokacin ma har da rugujewar gidaje,” inji shi.

Manajan Daraktan ya kwatanta shara da abu mai rai, kasantuwar idan tara ta kawai ake yi ba a kwashewa, to kara yawa da girma take yi. Amma idan ana kwasheta to ana rage mata karfi, inji shi.

Da yake mayar da jawabi, sakataren ‘yan kasuwar ‘Yan tifa, Malam Umar Shuwarin, ya ce suna iyakacin kokarinsu wajen kula da tsaftar kasuwar.

Duk da haka, kasancewar kasuwar a kan hanyar ruwan da ke gangarowa daga Fagoji da wani sashe na Unguwar Zai, ta sa ake samun matsala har ake ganin tamkar ba sa tsaftace muhalli.

Malam Umar ya zargi ma’aikata kwashe shara da kin zuwa su kwashe bola sai bayan an dade, a wani lokaci ma sai bayan an yi ruwa saman da  ya yi barna.

Shi ya bukaci gwamnatin jihar ta sa ma wa hukumar motocin kwashe shara, domin a cewarwsa hukumar na fama da karancin motocin da masu aikin kwasar sharar.

Ya ce suna bukatar karin albashi domin aikinsu yana da hadari sosai, musamman a wannan lokaci da ake fama da annobar coronavirus.