Notice: Undefined index: show_thumbnails in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 199

Notice: Undefined index: show_headline in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 200
Mourinho ba zai koma Real Madrid ba – Sergio Ramos - Aminiya
Aminiya

Mourinho ba zai koma Real Madrid ba – Sergio Ramos

Sergio Ramos

Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid da ke Spain, Sergio Ramos a ranar Talatar da ta wuce ya musanta rade-radin da ake yi na cewa Jose Mourinho zai koma kulob din.

Jose Mourinho wanda ya taba horar da kulo din Madrid bai samu wani kulob da zai horar ba tun bayan da Manchester United ta sallame shi a bara.

Ganin yadda kocin Madrid Zinedine Zidane yake fuskantar kalubale a bana, ya sa wadansu ke hasashen kulob din Madrid zai maye burgbinsa da Jose Mourinho.

Yanzu dai Ramos ya tabbatar Mourinho ba zai koma Madrid don ci gaba da horarwa ba hasali ma ya hori magoya bayan kulob din ne su ci gaba da mara wa Zidane baya don ganin ya samu nasara a kakar bana.

ADVERTISEMENT