✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mourinho na zawarcin dan kwallon Najeriya Bictor Osimhen

Sabon kocin Tottenham da ke Ingila, Jose Mourinho ya bayyana sha’awarsa ta sayo dan kwallon Najeriya Bictor Osimhen da zarar an bude kasuwar ’yan kwallo…

Sabon kocin Tottenham da ke Ingila, Jose Mourinho ya bayyana sha’awarsa ta sayo dan kwallon Najeriya Bictor Osimhen da zarar an bude kasuwar ’yan kwallo a watan Janairu mai zuwa. Yanzu haka Osimhen yana kwallo ne a kulob din Lille na Faransa.

Jim kadan bayan ya karbi jan ragamar kulob din a makon jiya Mourinho ya ce yana bukatar karfafa ’yan kwallon gabansa don haka ya karkata akalarsa ga Osimhen.

Osinhem wanda tauraruwarsa ke haskakawa a bana, yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles da koci Gernot Rohr yake gayyata kuma kawo yanzu ya zura kwallaye bakwai a raga a kaka ta bana a kulob din Lille.

Dan shekara 20 Bictor Osimhen yana daga cikin matasan ’yan kwallo da tauraruwarsu ke haskakawa a bana.

Idan za a tuna bayan ya karbi jan ragamar kulob din Tottenham, Mourinho ya dauko masu taimaka masa biyu daga kulob din Lille na Faransa da hakan ya sa ake ganin zai sake sayo Osimhen daga can.

Mourinho ya sanya hannu ne a kwantaragin shekara hudu a kulob din Tottenham.

A ranar Asabar da ta wuce ne ya lallasa kulob din West Ham United a wasansa na farko a gasar Firimiya.