✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mourinho ya zama mai sharhi kan kwallo

Tsohon kocin Manchester United  Jose Mourinho ya zama mai sharhi a kan wasannin kwallon kafa inda zai rika yin  sharhin kan gasar Zakarun Turai. Karo…

Tsohon kocin Manchester United  Jose Mourinho ya zama mai sharhi a kan wasannin kwallon kafa inda zai rika yin  sharhin kan gasar Zakarun Turai.

Karo na biyu ke nan da zai yi aikin da gidan talabijin na Rasha, bayan wanda ya yi a lokacin gasar cin Kofin Duniya da kasar ta karbi bakunci a bara kamar yadda BBC ya rawaito.

Gidan talabijin din ya sanar cewa Mourinho zai rika yi masa sharhin wasannin gasar cin Kofin Zakarun Turai da manyan batutuwan da suka shafi tamaula a duniya.

Tsohon kocin na Manchester United ya fara sharhin ne a wasannin da aka doka ranar Talata da wadanda aka a yi ranar Laraba kuma zai ci gaba har zuwa karawar karshe.

Mourinho ne ya jagoranci kungiyar Manchester United zuwa wasan zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai, daga baya ta sallame shi, bayan da ya kasa taka rawar gani ta kuma nada kocin rikon kwarya Ole Gunnar Solskjaer.