Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mourinho zai sake zama kocin Madrid

Shugaban kulob din Real Madrid da ke Sifen Florentina Perez ya ce ya kammala shirye-shiryen sake daukar tsohon kocin kulob din Manchester United Jose Mourinho a karo na biyu.

Mourinho dai ya taba horar da kulob din Madrid ne a shekarar 2010 zuwa 2013 kuma ya raba gari da kulob din ne a wancan lokaci saboda rashin kokari.  Kimanin mako uku ke nan da kulob din Manchester United da ke Ingila ya sallami Mourinho saboda rashin kokari amma abin mamaki rahotanni sun nuna Madrid tana yunkurin sake daukarsa karo na biyu don ya maye gurbin kocinsu na yanzu Santiago Solari.

ADVERTISEMENT

Mourinho wanda ya ki amincewa da tayin da kulob din Benfica da ke Fotugal ya yi masa na ci gaba da horarwa a can, alamu sun nuna zai karbi tayin da Madrid zai yi masa.

Sai dai rahotanni sun nuna da yawa daga cikin magoya bayan kulob din ba su ji dadin yadda mahukunta kulob din suke yunkurin sake daukar Mourinho a wannan lokaci da kulob din yake tangal-tangal ba.

ADVERTISEMENT

A halin yanzu dai kulob din Real Madrid yana matsayi na 5 a teburin gasar La-Liga ta Sifen bayan kulob din Real Sociedad ya doke Madrid da ci 2-0 a gida a karon farko cikin shekara 17.

Sai dai Amaju Pinnick ya ce idan Moses bai canja ra’ayi  ba, to Hukumar NFF za ta shirya masa wasan ban-kwana a matsayin karramawa.