Search
Subscribe
Msu kashe kansu kan bayyana shirinsu sai dai…

Msu kashe kansu kan bayyana shirinsu sai dai…

Kashi biyu cikin uku na wadanda suke kashe kansu masana sun ce suna ankarar da mutane cewa za su kashe kansu. Na yarda da wannan bincike nasu domin in ka bibiyi wadanda ke kashe kansu za ka iya fahimtar haka.

Sannan masana sun ce kashi daya cikin uku na masu kashe kansu suna fadar ta hanyar da za su hallaka kan nasu. Wannan ya sa na tuna da wani dattijo da ya kashe kansa a Jihar Kaduna. Kwana kadan kafin ya kashe kansa an ji yana fadin cewa shi fa ya gaji da duniyar nan. Kwana kadan da kalaman nasa ya sayo shinkafar bera ya sha, kafin a je asibiti rai ya yi halinsa.  Kusa-kusan nan wata budurwa a Zamfara mai suna A’isha da aka raba ta da saurayinta saboda ba ya da halin aurenta sai da ta ankarar da mutane cewa za ta hallaka kanta.

Shi ya sa na ce in ka ji mutum na fadin “Na gaji da duniyar nan… ko gara mutum ya mutu ya huta…” Alamu ne da ke nuni da cewa zai iya hallaka kansa, idan an ga gawarsa kada a yi mamaki.

’Yan makonni baya muna hira da wata yarinya sai take ce min ita fa ta gaji da duniyar nan, gara ma ta mutu ta huta, ita wallahi so ma take ta mutu. Kalamanta sun yi matukar ba ni mamaki tare da kada hantata domin na lura ba da wasa take maganar ba.

Da a ce zan bayyana wa ’yan uwanta halin da take ciki dariya za a yi mini, ko a ce min mai tsogumi. Ba wai fata nake ba, da a ce yanzu a ga gawarta, sai kuma in zo in fito ina ba da labarin yadda muka zanta da ita, laifina za a gani, a ce me ya sa ban sanar ba har sai da ta hallaka kanta?

Don haka a rika ankara duk lokacin da wani ya ce zai kashe kansa ko gara ya mutu ya huta.

 

Nasiru Kainuwa Hadeja (08100229688)

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin