✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu kiyayi kwari masu yada cututtuka

Wasu kwari na gida da na daji na daga cikin manya-manyan halittu masu yada mana cututtuka. Suna yin haka ne ta hanyoyi daban-daban yayin da…

Wasu kwari na gida da na daji na daga cikin manya-manyan halittu masu yada mana cututtuka. Suna yin haka ne ta hanyoyi daban-daban yayin da suka yi cizo ko kuma suka hau abin da mukan ci ko mukan sha. A masu cizon, wasu sukan sa mana kwayoyin cuta a lokacin da suka yi cizon, wasu su sa dafi (kamar kudan zuma), wasu kuma ba sa saka wata kwayar cuta illa dai su yi ta zukar jini har ma su iya sa ciwon karancin jini idan ba farga da wuri ba. Ya kamata mu san wadanne kwari ne wadannan domin mu guje su.

Bari mu fara duba masu yada cututtuka yayin cizo, kafin mu zo kan masu yada cututtuka ba tare da cizo ba, sai kuma mu karkare da masu cizo don kawai shan jini.

Sauro: Wato lange-lange mai ramar keta, shi ne babban mugun a cikin kwarin gida masu saka mana cututtuka. Kusan kowa ya san sauro shi yake kawo mana ciwon zazzabin Maleriya, wanda ke kashe miliyoyin mutane duk shekara, yawancinsu yara kanana. Abin da wadansu ba su sani ba dai game da sauro shi ne cewa ban da ciwon zazzabin Maleriya, zai iya sa ciwon zazzabin shawara na Yellow Feber da ciwon zazzabin zika, da ciwon zazzabin Dengue da ma wasu da dama. Don haka a kiyayi sauro.

Kudan Tsando: Wanda ake kira Tsetsefly, shi ma yana sa wa mutane da dabbobi musamman shanu a irin kasashenmu na Afirka cuta. Shi ya sa aka fi samun ciwon tsakanin makiyaya. Yana sa ciwon kwakwalwa na sammore da Fulatanci wato Sleeping Sickness da Inglishi, mutum ya ji ba ya tabuka komai sai yawan barci.

Kwaron Filfilwa: Wanda ake kira Blackfly ko Bakin Kwaro, shi an fi samunsa a kasashen Kudu, shi kuma ne ke sa ciwon dundumi (makanta) da tundurmi (kumburin kafa). Don haka duk wanda ya je kurmi cikin kungurmin dazukansu sai ya kiyaye cizon kwari don kada su sa masa irin wadannan cututtuka.

Kaska: Kaska ba dabbobi kadai suke wa barna ba. Kwari ne da kan sha jinin mutane tare da sa musu kwayoyin cuta daban-daban tun daga na bacteria har na birus irinsu zazzabin Typhoid da na ciwon Lyme wanda ke sa wasu irin kuraje.

Kuma: Kwari ne masu kama da kwarkwata, kuma su ma suna shan jini sosai. Su ake kira Flea da Inglishi. Kwari ne da ke yada cututtuka na bacteria masu sa annoba. Su aka alakanta da wata babbar annoba a tarihi (wadda aka kira Bubonic Plague) da ta yi sanadiyyar salwantar rayukan miliyoyin mutane a tarihi a yankin Nahiyar Turai shekaru dubu da suka wuce saboda suna bin beraye suna kwaso cututtukansu suna baza wa jama’a.

Sai kuma masu yada cututtuka idan suka taba kayan abincinmu su ne:

Kuda: Shi ne na biyu mai yada cututtuka da dama bayan sauro a irin kasashenmu masu zafi. Shi ne ummul-haba’isin cututtuka irinsu zazzabin Typhoid da ciwon amai da gudawa na kwalara da na atini.

Kyankyaso: Da dama ba a san cewa duka cututtukan da kuda kan iya yadawa kyankyasai ma za su iya yadawa ba, don haka a yi hankali sosai da kyankyasai.

Bari kuma a duba kwari masu shan jini, wadannan sun hada da:

Kwarkwata: Ba kamar kudin cizo da kwaron kazwa ba, kwarin kwarkwata za su iya kama kowa, mai tsabta da maras tsabta. Su ne kwarin da suka fi sa kaikayin kai ga yara ’yan mata, musamman ’yan makaranta, fiye ma da amosaninka, a wasu lokutan ma har da manya mata. Maza da yake a yanzu zamani ya zo muna yawan aske kawunanmu, an bar tara sumaAfro, abin ya yi sauki sosai a tsakaninmu. Kwarin sukan shiga kan yarinya ne daga wata zuwa maras ita, kamar a wurin wasa, kamar misali a zaman aji na makaranta ko ta musayar kallabi. Kwarin idan suka shiga kai jini suke zuka. Kusan a kididdiga, a duk yara mata goma sai an samu akalla daya mai kwarkawata, wato a a ji mai ’yan mata hamsin akan samu akalla biyar masu matsalar kuma ba wuya su sa wa na kusa da su.

Kudin Cizo: Su ne wadanda aka fi gani a kayan shimfida. Ana iya samunsu a kasashe da dama a duniya, tun daga kasashen nahiyar Amurka da nahiyoyin Turai da Asiya. Yawanci mutane ke yada su daga wannan wuri zuwa wancan a cikin jakunkuna da kayansu. Don haka ba abin mamaki ba ne a same su a gadon manya-manyan otal-otal, da na fitatttun wuraren shakatawa, kuma a iya kwasarsu a kai gida ba a sani ba. Abin da ya sa ake iya daukarsu da yada su shi ne cewa sun iya buya, domin da wuya a gansu da rana, don sukan iya shigewa cikin yadin katifa ko kalmasar zanin gado, ta yadda sai duhu ya yi kafin su lallaba su fito, su fara cizo suna shan jini. Wannan cizo zai iya sa wurin ya fara kaikayi ya canza kala, sai dai bai kai cizon kuma saka kaikayi ba. A kasashen Kudancin Amurka irinsu Medico, kudin cizo za su iya yada kwayoyin cuta masu sa ciwon sammore da muka yi magana da fari

Kwarin Kazwa: Kwari ne masu kama da kwarkwata ko kudin cizo, sai dai saboda kankantarsu, su ba a iya ganinsu da kwayar ido. Matsalar ita ce idan kwarin da ke kawo kazwa suka shiga gidan mutum, sai an yi da gaske kafin su fita, don haka za a ga ba mutum daya kawai sukan kama ba, kusan duk mutan gidan. Sun fi nunawa a yara saboda rashin karfin garkuwar jiki. Manya masu kwarin garkuwar jiki ba su cika nuna kuraje da kaikayi ba idan kwarin suka shiga karkashin fatarsu. Don haka su ma manya za su iya zama sila wajen yada wa yaransu wadannan kwari. Wato a wasu lokuta ba yara ne ke kwaso ciwon ba, manya ne ke yada wa yara. Kwarin kazwa kan iya kama kowane jinsi, fari ko baki, mai kudi da maras shi duka, sai dai ta fi kama maras shi inda akan samu cinkoson wurin kwanciya.

Masu sa dafi su kuma su ne irin su Kudan Zuma da Zanzaro da Kunama da Cinnaka da wasu nau’i na Gizo-Gizo, duk da cewa dai Kunama da Gizo-Gizo a kimiyyance ba kwari ba ne kuma su ne idan suka sa wa mutum dafi zai iya masa illa sosai idan ba a je asibiti da gaggawa ba.