✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu leka gidaje 60 da Khalifa Isyaka Rabi’u ya ba alarammomi 60

A 1986 ne, marigayi Khalifah Isyaka Rabi’u (Khadimul Kur’an) ya gina gidaje 60  a Unguwar Kofar Waika da ke Karamar Hukumar Dala a Jihar Kano…

A 1986 ne, marigayi Khalifah Isyaka Rabi’u (Khadimul Kur’an) ya gina gidaje 60  a Unguwar Kofar Waika da ke Karamar Hukumar Dala a Jihar Kano inda ya raba su ga alarammomi 60 don zama a ciki tsawon rayuwarsu. Aminiya ta gano marigayin ya gina gidajen ne daidai yawan Izifin Alkur’ani 60 a wani mataki na yi wa makaranta Alkur’ani gata da kuma cika burin mahaifinsa; Mun leka gidajen don ganin halin da suke ciki tare da mazaunansu:

 

Tsarin gidajen

A ziyarar da Aminiya ta kai Unguwar  Kofar Waika da ke birnin Kano, ta gano cewa an tsara ginin gidajen a layuka hudu, an kuma gina gidajen gaba da baya da kuma gefen dama da hagu na kowane layi.

Kuma tsarin ginin dukkan gidajen iri daya ne ma’ana gidaje ne ma’ana ba bene, sai dai wasu gidajen sun fi wasu yawan dakuna. Karami daga ciki shi ne mai daki da rumfa uku na daukar karatu da ban-daki da dakin girki, sai soro da kuma dakin saukar baki da ke zaure. Wasu gidajen kuma suna dauke da daki da rumfa hudu da ban-dakuna biyu da zaure. Haka kuma wasu gidajen alarammomin sun sanya rumfunan kwano a harabar gidajen wadanda almajiransu ke zama a ciki don daukar karatu tare da kwana a ciki,

Aminiya ta gano yawancin gidajen suna cikin kyakkyawan yanayi duk da cewa akwai wadanda fentinsu ya dauki tsawon lokaci ba a sabunta shi ba, wanda kuma binciken Aminiya ya gano hakan na faruwa ne dalilin bambancin karfin aljihun alarammomin.

Yadda aka samu gidajen

Dokta Yusuf Isyaka Rabi’u wanda aka fi sani da Gwani Lajin daya ne daga cikin ’ya’yan marigayi Khalifa Isyaka Rabi’u, kuma ya yi wa Aminiya karin haske kan tarihin samuwar gidajen inda ya ce mahaifinsu ya gina gidajen ne a kokarinsa na yi wa Alkur’ani hidima a gefe guda kuma wani mataki ne don cika burin mahaifinsa. “Khalifa ya ba mu labarin cewa lokacin da suke Unguwar Jingau inda mahaifinsa Malam Rabi’u ke karatu da almajiransa, akwai wata mata da take sana’ar tuyar kosai sai ya zamo idan suna karatu hayakin itacen da take amfani da shi yana damunsu. Sai shi Malam Rabi’u yake cewa idan Allah Ya yarda zai koma bakin Gwauron Dutse ya gina tsangayarsa shi da almajiransa yadda za su zauna ba tare da wani ya dame su ba. Daga baya kuma sai Khalifa ya yi gida a Jakara suka koma har kuma daga baya Allah Ya nufa ya samu wannan filin na Gwauron Dutse ya gina. Sai bayan da Khalifa ya gina gidansa ne sannan ya tuna da waccan magana ta mahaifinsa, don haka sai ya himmatu wajen samar da wadancan gidaje a matsayin tsangayar da mahaifinsa ya ci burin samarwa wanda kuma aka gina su a bayan gidan da Khalifan ya zauna har lokacin rasuwarsa,” inji shi.

Dokta Yusuf ya ce mahaifinsu ya gina gidajen 60 daidai da yawan Izifin Alkur’ani duk da cewa ba a wuri daya aka gina gidajen duka ba. “Da aka samu filin sai aka fara ginin gidajen da niyyar sama wa kowane Izifi guda na Alkur’ani gida don haka aka so a samu gidaje 60. Da aka fara ginin an samu kamar gidaje 50, to saboda wasu dalilai ba a samu an karasa ragowar 10 a wannan wuri ba, sai lokacin da aka gina Masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani a Kofar Mata aka gina sauran gidajen a wancan wuri, Don haka 60 din suka cika kamar yadda ya yi niyya tun farko.”

Yadda ake bada gidajen

Dokta Yusuf Rabi’u ya ce kamar yadda mahaifinsu ya tsara an bayar da gidajen ne ga mahaddata Alkur’ani kuma har yanzu akan bayar da gidajen ga irin wadanan mutane. “Da aka gina gidajen sai aka bar su a matsayin khubusi, aka ba mahaddata Alkur’ani da niyyar su zauna a ciki tsawon rayuwarsu. Idan aka samu wanda yake ciki ya rasu sai a samu wani daga cikin ’ya’yansa wanda shi ma mahaddaci ne a ba shi gidan a hannunsa. Wannan ya zama zaburarwa ga ’ya’yan alarammomin suna mayar da hankali kan karatun Alkur’ani don su ma so su ci gaba da zama a gidajen. An taba samun wani alaramma da ya zauna a cikin irin wannan gida amma da yake bai taba haihuwa ba,  da ya rasu sai aka bayar da gidan ga wani alaramman daban,” inji shi.

‘Yadda na samu nawa gidan’

Malam Sani shi ne Ladanin Masallacin Sheikh Muhammad Rabi’u da ke Gwauron Dutse, kuma daya ne daga cikin alarammomin da ke zaune a cikin gidajen da marigayi Khalifah Sheikh Isyaka Rabi’u ya gina. Ya ce samun gidan da yake ciki wani cika alkawari ne da marigayi Khalifa ya sha yi masa. “Lokacin da aka fara rarraba gidajen ba na cikin wadanda suka samu, amma bayan da Allah Ya yi wa wanda ke cikin gidan rasuwa kuma ya kasance bai taba haihuwa ba, sai aka ba ni. Ina ganin samun gidan nan nawa Allah ne Ya cika alkawarin da Khalifa da ya yi min a baya. Don koyaushe muka zauna da marigayi Khalifa yakan yi min alkawarin sama min gidan da zan zauna.”

Yadda ake kula da gidajen

Game da yadda ake kula da gidan, Babban Ladanin ya ce yawancin lokaci mutanen da ke zaune a gidajen ne ke gudanar da gyare-gyaren gidan, duk da cewa a lokacin da Khalifa ke raye yakan gudanar da wasu ayyukan da kudinsa. “Na san dai lokacin da Khalifa yana raye yakan turo a duba halin da gidajen ke ciki inda kuma yakan dauki nauyin gudanar da gyare-gyaren da gidajen ke bukata daga aljihunsa. Haka mu mazauna gidan muna yin duk wani abin da ya kamata maigida ya yi wa gidansa. Ai ma da kunya a yi maka irin wannan gata sannan duk wani karamin abu ka dauka ka tafi kana neman a yi maka. A gaskiya muna yin duk wasu abubuwa da ba su fi karfinmu ba domin mu muke zaune a cikin gidajen mu ne muke morar gidan ba wani ba,” inji shi.

Yadda ake gudanar da rayuwa a gidajen

Malam Bala Mika’ilu ya ce yanayin rayuwar da suke gudanarwa a gidajen rayuwa ce ta makaranta wacce ke cike da harkar karatun Alkur’ani. “Rayuwa ce ta almajirci domin yawanci rayuwar da muka gada daga iyayenmu ke nan. Kusan kowane gida za ki ga ana gudanar da makaranta. Kuma kin san rayuwar almajirci dole a kewaye muke da almajirai wadanda ke kwana tare da mu. Duk da cewa rayuwarmu gaba daya ta dogara ce a kan karatu amma hakan bai hana mu gudanar da wasu sana’o’in ba. A cikinmu akwai ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu. Akan wannan tsarin muka dora almajiranmu,  almajiranmu ba sa bara. Domin lokacin da Khalifa yake raye yana taimaka mana da abinci da suttura kai har da tsabar kudi domin gudanar da harkar almajirai. A yanzu ma da ya rasu wadansu daga cikin ’ya’yansa suna yi mana, alhamdulillah! A wannan lokaci kuma za ki samu almajiranmu suna samun abinci daga gidajen da suke aikatau. Idan an tashi makaranta. Kowane muna kula da irin abin da yake aiwatarwa domin wadannan ’ya’yan amana ce a wurinmu,” inji shi.

‘Yaranmu suna zuwa makarantar boko’

A cewar Malam Bala duk da cewa sun tashi a gidan makaranta, hakan bai hana su sanya ’ya’yansu a makarantun boko ba. “Kin ga bayan karatun Alkur’ani dukkan ’ya’yanmu suna yin karatun boko. Ba mu yarda an bar mu a baya ba. ’Ya’yana suna manyan makarantu da sauransu. A yanzu har makarantar zamani na bude wacce muke koyar da ilimin addini da na boko,” inji shi.

Shi ma Alaramma Abubakar Ibrahim da ke cikin wadanda suka amfana da gidajen ya ce ya shafe shekara 40 a cikin gidan wanda kuma yake gudanar da harkar makaranta a ciki, sai dai zuwa yanzu saboda yanayin girma ya sa ya daina gudanar da harkar almajirci. “Na shafe shekara 40 a cikin wannan gida. Ina zaune da matana da ’ya’yana. Da farko na yi harkar makaranta tare da almajiraina amma yanzu saboda girma ya kama ni ga shi kuma koyaushe ina fama da rashin lafiya ya sanya na daina harkar makaranta. A takaice ba ni da almajiri ko daya. ’Ya’yana kuma a yanzu duk suna makarantar boko don haka ba za su iya gudanar da harkar almajiirai ba, kin san ita harkar almajirai akwai wuya a ciki,” inji shi.

Alarammomin da Aminiya ta tattauna da su sun yi kira ga masu hannu da shuni da sauran jama’a su yi koyi da marigayin lura da cewa shi kadai ne ya gina irin wadannan gidaje. “Idan da za a samu mutane suna yin irin wannan aiki da marigayi Khalifa ya yi wallahi da an rage matsalolin rayuwa a cikin al’umma. A iya sanina irin wadannan gidajen su kadai ne a Jihar Kano, bayan akwai mabukata akwai kuma masu halin da za su iya. Allah Ya taimake su Ya sa musu tausayi da jinkai irin na marigayi Khalifa,” inji su.