✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

“Mu muka kashe ’yan canjin da muka yi garkuwa da su”

Wasu mutune uku da a yanzu haka suke tsare wurin ’yan sanda, wadanda ake tuhuma da kisan wasu masu sana’ar canjin kudi, Alhaji Yakubu Musa…

Wasu mutune uku da a yanzu haka suke tsare wurin ’yan sanda, wadanda ake tuhuma da kisan wasu masu sana’ar canjin kudi, Alhaji Yakubu Musa da Alhaji Hassan Ummaru a Unguwar Okorodu da ke Legas kimanin wata daya da ya wuce sun tabbatar da cewa sun kashe wadanda suka yi garkuwa da su ne domin su kauce wa kamun hukuma.

Wadanda ake zargin, Olwatosin Olanrewaju mai shekaru 40 da Mayowa Olawuni wanda aka fi sani da Janaral da kuma Babatunde Idris wanda aka fi sani da Aloma sun bayyana yadda suka kitsa sace ’yan canjin ta hanyar yaudarar su a kan za su canza masu kudi Dala $10,000 zuwa Naira, inda daga baya za su kame su kuma su nemi iyalansu da su biya su kudin fansa.

“Tabbas mun kasha ’yan canjin ne saboda muna tsoron kada bayan mun sako su su ba ’yan sanda wasu muhimman bayanai da za su sanya a kama mu,” inji Babatunde Idris.

Ya ci gaba da cewa tun farko, tunanin kitsa yadda za su sace duk wani dan canji da kaddara ta fada ma wa sannan su nemi iyalansa su biya kudin fansa ya zo masu ne sakamakon fadan da suka yi da wasu ’yan wata kungiyar asiri mai suna Eiye Confraternity, wacce suke adawa da tasu kungiyar a cikin watan Maris day a gabata, a Unguwar Abraham Adesanya yankin Ajah, Legas. Kamar yadda ya bayyana, a wannan fada da suka yi, shida daga cikin ’yaýan Eiye ne suka sheka barzahu, yayin da wasu da dama suka samu raunika.

“Bayan mun kashe su sai muka ga akwai bukatar mu samu kudi don mu dan buya zuwa wani lokaci, don haka a cikin irin tattaunawar da muke yi ne sai dabarar yadda za mu sace masu sana’ar canji ta fado mana. Da farko mun yi niyyar yin kan mai uwa da wabi ne ga ’yan canjin, inda daga karshe kaddara ta fada kan Hassan da Yakubu muka same su.

“Daga nan ne sai muka kira su a waya, muka fada masu cewa akwai wani abokinmu ya dawo daga Amurka kuma yana son su canza masa Dala $10,000. Da jin kudin sai suka nuna sha’awarsu amma kuma sun dan nuna jin tsoron zuwa inda muke. Amma mun yi nasarar ciwo kansu bayan da muka tabbatar masu da cewa za a yi komai a banki ne.

“Mu da su muka amince mu hadu a wani banki a Ikorodu, inda da suka zo sai suka shiga cikin motarmu muka fara tattaunawa. Daga nan kuma sai suka bukaci suna son ganin dalolin, sai muka fada masu yanzu shi abokin namu da ya zo daga Amurka zai zo da su. Bayan an dauki lokaci bai zo ba sai kuma muka fada masu gara mu je tare da su mu dauko shi tunda da alama zai bata mana lokaci. Haka suka amince muka ja mota muka tafi.”

Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas, Bala Elkana, a wani taro da manema labarai ya bayyana cewa ’ya sanda sun gano gawarwaki hudu a cikin wani ramin masai wanda kuma biyu daga cikinsu na ’yan canjin da suka bata ne.

Elkana ya ci gaba da cewa a ranar 4 ga watan Maris day a gabata, kimanin karfe 5:30 na yamma Hukumar ’yan sanda ta Jihar Legas ta samu koke daga Ikorodu, cewa wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kira wani Alhaji Yakubu Musa da Alhaji Hassan Ummaru wadanda suke sana’ar canjin kudi a Layin Benson da ke Ikorodu suka fada masu cewa suna da wani dan uwa, wanda ya dawo daga waje kuma yana son ya sayar da Dalar Amurka $10,000.

Kamar yadda ya fada a da sun ce za a yi cinikin ne a banki amma bayan sun zo bankin sai suka yi wani waje da su kuma suka fara kiran abokansu da iyalansu suna neman a biya su kudin fansa.

Kamar yadda ya bayyana, duk da yake iyalansu sun biya har Naira milyan daya da dubu dari shidda ga wadanda suka yi garkuwa da su, sun ki su sako su kuma daga nan ba a sake jin duriyarsu ba.