✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu nazarci wasu sinadaran kyautata rayuwa (1)

Jama’a, Assalamu alaikum. Yau ma dai Allah Ya sake sada mu da ku a wannan muhimmin shafi na Sinadarin Rayuwa, inda kamar yadda kuka sani,…

Jama’a, Assalamu alaikum. Yau ma dai Allah Ya sake sada mu da ku a wannan muhimmin shafi na Sinadarin Rayuwa, inda kamar yadda kuka sani, muke zakulo da binciko wasu sinadarai da ke yaukaka mana rayuwarmu ta yau da kullum, domin mu dace da samun kyakkyawar rayuwa. A yau kuma mun samo wasu sinadarai ne da ya kamata mu maida hankali a kansu, domin su zame mana jagora, ta yadda za mu kara inganta al’amuran rayuwarmu.

Da farko dai za mu fara duba wadansu muhimman abubuwa ne guda hudu, wadanda suke gajiyar da jiki, suke lalata shi, sannan su haifar wa mutum cikas a rayuwarsa. Ke nan, wadannan abubuwa hudu, za mu yi kokarin kauce musu ne, idan dai har muna son cimma ingantacciyar lafiya ga jikinmu.

Abu na farko da za mu koya wa kanmu kaurace mawa shi ne yawan surutu. Kamar yadda muka sani, shi baki an yi shi ne saboda biyan wasu muhimman bukatu na rayuwa, cikinsu kuwa har da yin magana. Sai dai abin da ya kamata mu sani shi ne, ba kowace magana ce ta kamata mu rika yi da bakunanmu ba. Kamata ya yi duk maganar da za mu yi ta kasance wacce za ta amfanar da mu ko waninmu ce. Ke nan, ba za mu maida kanmu kamar kanari ba, mu yi ta magana cacacai-cacacai a kowane lokaci ba. Mu san da cewa komai ya yi yawa yana zama aibu ne, don haka, yawan magana, musamman marar amfani ba ta da wata fa’ida ga rayuwarmu. Idan har ka san cewa babu dalilin da za ka yi wata magana, yin shiru da bakinka shi ya fi amfani. Domin kuwa bakin naka zai huta, gabobin cikin bakin ma za su huta, sannan kwakwalwarka, wacce ita ce za ta yanko tunanin abin da za ka fada, ita ma za ta huta.

Wani dalili kuma da ya sanya ya kamata mu kaurace wa yawan magana ko surutu shi ne, domin kauce wa maganganun banza, wadanka za su iya jawo tashin hankali ko kuma su cutar da al’umma. Abin da kowa ya sani shi ne, duk wani mutum mai yawan surutu yakan kasance mai karya, domin a duk lokacin da ya rasa abin da zai fada, saboda ya saba da surutu, sai kawai ya kirkiro abin da babu shi ya fada, domin dai ya samu abin magana. Ta haka, yana iya kirkira kazafi ko maganganun cin mutuncin wani, ya fada. Idan haka ta faru kuwa, shi ke nan jidali ya samu, domin wanda aka yi wa karyar ko kuma aka yi masa kazafi ko bata suna, kila ba zai iya daurewa ba. Allah kadai Ya san abi da zai biyo bayan wannan. Ashe ke nan, rashin surutu na taimakawa wajen hutar da baki da hutar da kwakwalwa da kuma hutar da haifar da tashin hankali da faruwar mugayen al’amura.

Abu na biyu da ya kamata mu kaurace mawa shi ne yawan barci. Rayuwar kadaran-kadahan ita ce mai matukara amfani ga dan Adam. A komai za ka yi, kada ka sake ka ce za ka zake, kuma kada ka ce za ka yi kwauro. Yawan barci na daya daga cikin abubuwa masu cutar da jikin dan Adam, domin kuwa likitoci ma sun tabbatar da haka. Yawan barci na haifar da kasala, yana haifar da kyuya, sannan kuma yana lalata dukkan gangar jiki. Ke nan ya kamata mu san tsawon lokacin da ya kamata mu rika yin barci, sannan mu san lokacin da za mu tashi domin gudanar da wasu ayyuka na ci gaban rayuwarmu. Amma mutum kullum a kwance kamar kasa? Wannan bai dace da kiwon lafiyar jikin dan Adam ba.

Sai kuma abu na uku, wanda ya kamata mu kaurace mawa domin sama wa jikinmu cikakkar lafiya da kulawa. Wannan kuwa shi ne yawan cin abinci fiye da kima. Babu shakka, yawan cin abinci ba karamar illa yake haifarwa ga jikin dan Adam ba. Kamar yadda Shugaban Annabawa ya gaya mana, ya ce ya kamata ne mutum ya raba cikinsa zuwa kashi uku. Watau kashi guda domin cin abinci, kashi guda domin ruwa, sai kuma kashi guda na iska, watau na shakar iska. Haka kuma, ya ce mana mu rika cin abinci a lokacin da muke bukatarsa kawai, watau bayan mun ji yunwa ke nan. Babu wata fa’ida ko amfani ga mutum ya rika cin abinci a kowane lokaci.

Akwai hikima mai yawa da fa’ida mai yawa ga mutumin da ya tsara yadda zai ci abinci ba tare da ya wuce kima ba. Jikinsa zai kasance cikin lafiya, saboda cikinsa da sauran mukarraban da ke tafiyar da sarrafa abincin jikinsa za su samu isasshen hutu da lokacin aikinsu. Amma idan mutum ya rika cin abinci fiye da kima, za su gaji, za su kasa gudanar da aikinsu yada ya kamata. Wannan zai sanya mutum ya zama cikin kasala, sannan haka na iya haifar masa da cutuutuka masu yawa. Idan haka ta faru, ke nan jikin mutum ya shiga kaka-ni-ka-yi ke nan.

Abu na hudu da ya kamata mu lizimta kuma shi ne, mu takaita ganawa da mutane barkatai a lokaci guda. Watau kada mu kasance kowa da ruwanmu da shi, da mutumin kwarai da gurbatacce. Idan haka ta faru, za mu kasance cikin gajiya, sannan kuma za mu kasance cikin tarayya da wadanda ba su dace ba. Abin da ya kamace mu shi ne, mu zama masu tarayya da mutanen kwarai, masu hikima da basira. Mu kasance tare da mutanen kirki ba shashashai da wawaye ba.

Babu shakka, dan Adam yana koyon al’amura ne daga mutanen da yake tare da su. Idan yana tare da mutanen kwarai, lallai kam zai kasance mutumin kwarai. Haka kuma idan yana tarayya da mutanen banza, komai daren dadewa, shi ma yana iya zama mutumin banza, koda kuwa a baya ya kasance mutumin kirki. Masu hikimar magana ma sun ce, zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai.

Wadannan abubuwa guda hudu da muka zayyana, ya dace mu lizimce su, mu dabbaka shawarwarin nan domin samun dacewa da ingantaccen jiki mai lafiya, ta yadda za mu ci ribar lafiyar jikinmu, amin. Watau ke nan mu kaurace wa yawan surutu marar amfani, mu kaurace wa yawan barci, mu kaurace wa yawan cin abinci ba kan gado; sannan kuma mu takaita yawan mutanen da za mu rika ganawa ko mu’amala da su. Allah Ya sa mu dace, amin.

Za mu ci gaba