Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mu rika yi wa shugabanni addu’a  maimakon la’anta – Rabaran Tutu

Rebaran Haruna Tutu

Rabaran Haruna Tutu shi ne Shugaban Cocin Assemblies of God na Gundumar Saminaka da ke Jihar Kaduna. Kuma wakilin Shugaban Cocin Assemblies of God na Najeriya a yankin Arewa maso Yamma. A tattaunawa da wakilinmu kan zabubbukan da suka gabata, ya bukaci a yi wa shugabannin da aka zaba addu’a. Kuma ya bukaci shugabannin da aka zaba, su ji tsaron Allah su kyautata wa al’ummar kasar nan. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

ADVERTISEMENT

Ganin cewa an yi zabubbuka a kasar nan kwanakin baya, me za ka ce kan yadda aka yi zabubbukan. Kuma wadanne shawarwari  za ka ba  shugabannin da sauran jama’ar kasar nan?

Muna godiya ga Allah kan yadda aka kammala zabubbukan kasar nan lafiya. Babu shakka kafin a yi zabubbukan an samu fargaba kwarai da gaske, amma Allah cikin ikonSa Ya sa aka yi zabubbukan lafiya saboda haka muna godiya ga Allah.

ADVERTISEMENT

Sannan muna kira ga jama’a su rungumi gwamnatin nan da aka zaba. Domin Allah ne Mai bayar da shugabanci. Kuma  wannan abu ne na ra’ayi kowa yana da nasa ra’ayin.  Lokaci ya yi da kowa yake duba cancanta. Ka ga a nan sai mu ce abin da aka yi, kan wannan zabe zabi ne na jama’a. Wato jama’a ne suka dubi cancanta, tun daga sama har kasa.

Saboda haka muna kira ga jama’a a zauna lafiya, a bai wa shugabannin da aka zaba goyon baya da hadin kai, domin a samu zaman lafiya da ciyar da kasa gaba. Idan babu zaman lafiya da hadin kai, komai ba zai yiwu ba.

Shugabannin da aka zaba a yi musu addu’a Allah Ya ba su basira da hikima, kuma Ya ba su zuciya ta tausaya wa al’ummar kasa baki daya.

Don haka ina kira ga jama’a musamman malaman addinan nan biyu, wato Kiristanci da Musulunci mu yi addu’a. Muna da babban aiki a gabanmu kan mu yi addu’a domin shugabanninmu da jama’a suka zaba. A daina la’antar shugabanni a daina zaginsu. Idan muka yi haka, sai Allah Ya la’ance su su ba mu wahala. Amma idan muka yi musu addu’a, sai Allah Ya daidaita su.

Su kuma shugabannin da aka zaba, tun daga kan Shugaban Kasa da wakilan majalisun tarayya da gwamnoni da wakilan majalisun jihohi su sani cewa su wakilai ne na al’umma. Kuma kamar yadda aka koya mana a cikin Littafi Mai tsarki yayin da adalai suke mulki, al’umma sukan yi farin ciki da murna. Kuma yayin da mugaye suke mulki, al’umma sukan yi kuka. Ba abin da muke bukata ba ke nan.

Don haka muna son mu ji jama’a suna murna da farin ciki. Don haka shugabannin nan da aka zaba su bai wa jama’a hakkinsu, idan aka bai wa jama’a hakkinsu za a zauna lafiya. Wadannan shugabanni su nemo duk hanyoyin da za su samar wa jama’a ayyukan yi. A biya wa manoma bukatunsu a gyara hanyoyin kasar nan, a gyara asibitoci a samar da ruwan sha, idan aka yi haka talakawa za su manta da gwamnati su rungumi abubuwan da suka sanya a gaba. Babu wanda zai yi kukan  cewa ba a yi masa komai ba.

Wato shugabanni su yi wa jama’a adalci shi ne abin da Allah Ya ce a yi. Babu son kai babu nuna bambanci, idan aka yi haka za a zauna lafiya.

Kuma ina addu’ar Allah Ya bai wa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i nasara da hikima da ikon aiwatar da akidunsa masu kyau a Jihar Kaduna.  Kuma ina kira ga jama’ar jihar kan su ba shi goyon baya da hadin kai.

Ana fama da masu garkuwa da mutane a kasar nan, musamman a Jihar Kaduna, a matsayinku na shugabannin addini, wadanne hanyoyi ne kake ganin za a bi a magance matsalar?

Matsalar garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen jama’a da suke faruwa a kasar nan akwai damuwa kwarai da gaske. Babu shakka tsaro babban nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati. Amma ba gwamnatin kadai ba, har  da dukkan sauran al’umma. Wato kowa yana da rawar da zai iya takawa. Ita gwamnati ita ce take da jami’an tsaro idan ta tanadar wa jami’an tsaron nan dukkan abubuwan da suke bukata, wajibi ne su sauke dukkan hakkin da ke kansu na tsare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

Babbar damuwa ce a wannan kasa musamman a Jihar Kaduna. Domin muna jin abubuwan da suke faruwa a hanyar Kaduna zuwa Abuja da hanyar Birnin Gwari, inda ake yin garkuwa da jama’a ana karbar kudade, wadansu ma ana kashe su a kwace duk kadarorin da suke da shi. Wannan babbar damuwa ce kwarai da gaske.

Don haka muna kira ga gwamnati ta tashi tsaye ta yaki wannan babbar annoba da ta taso mana.

Mu kuma malaman addini mu tashi tsaye mu ci gaba da yin addu’o’i mu roki Allah Ya yaye mana wannan mummunar annoba da ta taso mana.

Gwamnati ta bai wa jami’an tsaro abubuwan da suka kamata domin su magance wannan annoba. Idan aka yi haka za a samu nasarar kawar da wannan annoba.

Kamar a Karamar Hukumar Lere mun ga irin gudunmawar da wadansu jama’a suka bayar da kuma addu’o’in da muka yi wajen kawar da wannan annoba. Don haka muna fatar haka ta faru a Jihar Kaduna da Najeriya baki daya.

A yanzu damina ta fara nuna alamar faduwa a wani yanki na Arewa, ko kana da sako ga manoma da gwamnati?

Babu shakka alamu sun fara nuna damina ta kusa faduwa a yankin Arewacin kasar nan. Don haka wannan lokaci ne da ya kamata kowanne manomi ya tashi ya yi shirye-shiryen da suka kamata.

To, amma mun san akwai karancin kayayyakin aikin gona kuma suna daga cikin abubuwan da suka kamata gwamnati ta tashi tsaye ta samar da wadannan kayayyaki. Domin idan aka ba manomi kayayyakin aiki kamar taki da iri da maganin kashe ciyawa da taraktocin noma an yi masa komai, kuma zai yi godiya.

Bayan haka ina kira ga gwamnati bayan manoma sun noma kayayyakin amfanin  gona  ta tashi tsaye ta sayi rarar amfanin gonar da manoma suka noma, domin kada manoma su rika yin asara. Musamman a bana manoma sun samu amfanin gona amma yanayin da takin zamani yake a yanzu babu manomin da zai bugi karji ya ce noman da ya yi a bara zai kwatanta a bana. Amma idan gwamnati ta tashi ta taimaka wa manoma da kayayyakin aikin gona za a yi noma.

Idan manomi ya kai amfanin gona kasuwa ya sayar ya zo ya iya biyan abubuwan da ya kashe noman zai yi gaba. Don haka muna kira ga manoma su tashi tsaye ita kuma gwamnati ta tallafa musu da kayayyakin aiki kuma ta rika saye rarar kayayyakin amfanin gonar da suka noma.

Kuma ya kamata masu hali su rika bude kamfanonin sarrafa kayayyakin amfanin gona a kasar nan.  Misali a Karamar Hukumar Lere duk noman da ake yi, a ce babu wani kamfanin sarrafa kayayyakin amfanin gona, sai dai a fitar da wadannan amfanin gona zuwa wasu wuraren. Wannan babbar damuwa ce domin babu karfafa wa manoman a wannan yanki.

Don haka idan ana son a karfafa wa manoman wannan yanki gwiwa a kawo wani babban kamfani na sarrafa kayayyakin amfanin gona yin haka zai taimaki manoman yankin da Jihar Kaduna da Najeriya baki daya.

Karshe wane sako kake da shi ga al’ummar Najeriya?

Sakona ga al’ummar kasar nan shi ne mu hada kai, mu rungumi juna mu zauna lafiya da junanmu. Mu kawar da bambance-bambancen addini da kabilanci, mu yi aiki da zuciya daya domin ci gaban kasarmu.