Da Dumi Dumi

Mu ruga mu bar makiya ruga

Har yanzu ana ci gaba da cece-ku-ce game da yunkurin da Gwamnatin Tarayya take yi na samar da gandun kiwo mai  suna RUGA wanda matsin lamba ya tilasta wa gwamnatin jingine tsarin.

Gwamnati dai ta fito da tsarin ne da nufin samar da gandun kiwo irin na zamani domin bunkasa harkar kiwon dabbobi kowane iri, kuma tsarin zai amfani duk wani mai kiwo ne daga kowace kabila ya fito, ba lallai sai Bafulatani ba, amma saboda an sanya wa gandun kiwon suna RUGA sai ’yan adawa suka samu kafa suka rika sukar tsarin suna cewa Shugaba Buhari ya fito da tsarin ne domin dadada wa ’yan uwansa Fulani kawai, shi ya sanya aka sanya wa shirin suna RUGA, wanda ya sanya saboda yawan suka dole Gwamnatin Tarayya ta jingine tsarin da nufin kara nazari.

Wadannan ’yan adawa su ne suke kwazzabar Fulani makiyaya, inda suke zarginsu da laifin da suka aikata da wanda ba su aikata ba, suna yin haka ne da nufin bata sunan Fulanin domin su shafa musu kashin kaji don kowa ya kyamace su, yadda za su zama tamkar mujiya a cikin tsuntsaye.

A kwanan nan aka kashe Funke Olakunri ’yar Shugaban Kungiyar Kare Muradun Yarbawa wato Afenifere, Mista Reuben Fasoranti, kuma nan take shugabannin yankin Kudu maso Yamma suka fito suka dora allhakin kisan a kan Fulani makiyaya. Duk da cewa binciken jami’an tsaro ya nuna cewa wadansu ’yan ta’adda ne suka kashe ta kuma ana ci gaba da bincike, amma shugabannin kabilanci na yankin suka ki yarda, sai ci gaba suke yi da kwazzabar Fulani makiyaya tare da yin kalamai masu tayar da hankali yadda za su tunzara mutanensu su tayar da hankali saboda kasar ta rikice.

Haka kuma duk lokacin da aka samu rahoton yin garkuwa da mutane a yankin Yarbawa sai a ce Fulani ne, ba tare da wani bincike ba. Akwai wani dan kabilar Yarbawa daga Jihar Ondo da ya bayar da labarin cewa wadansu mutane sun tare su a kan hanya suka iza keyarsu cikin daji, kuma ba Fulani ba ne, amma sai suka yi sa’a wani yaro Bafulatani ya ga abin da ya faru da su, sai ya je ya fada wa ’yan uwansa, su suka je suka tarwatsa wadanda suka yi garkuwa da su din, suka kwato su, suka koma da su har wurin da motarsu take.

ADVERTISEMENT

Kodayake ana samun Fulani a cikin harkar garkuwa da mutane, amma sun fi aikata wannan ta’asar a yankin Arewacin kasar nan, amma da yake ana so ne a bata sunan Fulani sai ya kasance a duk inda aka yi garkuwa da mutane a kasar nan sai a laka wa Fulani laifin.

Saboda a samar da mafita game da yawan rikicin manoma da makiyaya ne gwamnatin Shugaba Buhari ta yi yunkurin samar da gandun kiwo da ake kira “Cattle Ranch” sai ’yan adawa suka ce ba su yarda ba, aka sake fito da wani tsarin mai suna “Cattle Colony” nan ma suka ce ba su amince ba, yanzu an fito da tsarin makiyaya mai suna RUGA suka sake tsalle waje guda suka ce ba su yarda ba.

Wato dai su wadannan ’yan adawar ba su kaunar duk wani kokari da za a yi domin rayuwar Fulani makiyaya ta inganta, so suke yi a bar su su yi ta gararamba, suna fama da yunwa da talauci da jahilci, yadda za a yi ta dora musu karan-tsana.

Duk wata sana’a gwamnati tana taimakawa wajen ingantata, shi ya sanya ake da ma’aikata guda mai kula da harkar noma, amma saboda ba a so rayuwar Fulani ta inganta sai aka yi kokarin soke Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi, batun kiwo sai ya koma karkashin Ma’aikatar Gona, maimakon ya samu ma’aikata ta kashin kansa.

Yanzu kiwo ba na Fulani ba ne kawai, kabilu da dama sun shiga harkar kiwo, hasali ma dai mafi yawan shanun da Fulani ke kiwo ba nasu ba ne, na wadansu hamshakan mutane ne. Su Fulani kiwon dabbobin kawai suke yi, wato mai doki ya koma kuturi ke nan. Amma duk da haka ’yan adawar nan ba su jin tausayin Fulani saboda mayuwacin halin da suke ciki, sun fi so sun gansu cikin wahala tun da kabilarsu daya ce da Shugaban Kasa.

An fake da Fulani makiyaya ne kawai ana yaki da Arewacin Najeriya yadda za a gurgunta duk wani shiri da zai haifar da ci gaban yankin, saboda haka ya kamata ’yan Arewa su farka su bude idanuwansu su gane masu kaunarsu da kuma makiyansu, idan zaben shekarar 2023 ya zo su yi amfani da kuri’unsu wajen yakar duk yankin da ya yi adawa da tsarin gandun kiwo da ake kokarin samarwa. Duk yankin da ya yaki tsarin samar da gandun kiwo na RUGA su ruga da gudu su bar shi a lokacin zabe mai zuwa. Saboda haka batun mayar da mulki yankin Kudancin kasar ba ta taso ba, kowa ya fito ya nema, wanda yake da rinjaye ya dauka, babu wani batun karba-karba, domin dimokuradiyya tsantsa ba ta san da tsarin karba-karba ba ,  mafi rinjaye shi ke da mulki.

Na ji dadi da gwamnonin wasu jihohin Arewa suka nuna aniyarsu ta rungumar tsarin gandun kiwo na Ruga, inda har suka nuna cewa tuni har sun samar da fili domin aiwatar da shirin, abin da ya kamata sauran jihohin Arewa su yi ke nan, domin shiri ne mai dimbin amfani.

Duk wani shiri da yankin Kudancin kasar nan ke adawa da shi idan aka yi nazarinsa sosai za a tarar cewa sun ga zai amfani al’ummar Arewa ne, ko da kuwa sun amince cewa shiri ne mai kyau da zai amfani kowa da kowa a kasar nan. Su yankin Arewa ne ba su son ganin ya bunkasa, sai dai ya zauna a matsayin kurar-baya.

Ya kamata Fulani makiyaya su yi wa kansu fada, su guji bai wa makiyansu kafar da za su samu nasara a kansu, domin ana yi musu gadar-zare ne su kuma suna kokarin hawa ta hanyar shiga harkar ta’addanci. Su yi kokari su hada kawunansu domin su fuskanci kalubalen da ke fuskantarsu.

Su kuma Fulani makiyaya da ke Kudancin kasar nan su daure su bar yankin su dawo jijohin Arewa da za a bude makiyaya na zamani domin su huta tare da dabbobinsu ba tare da fuskantar tsangwama ba. Babu amfani su zauna a wurin da ake yi wa rayukansu da na dabbobinsu barazana a kullum. Lokaci ya yi da za su zauna a wuri guda su huta, su samu ilimi kuma a kula da lafiyarsu da na dabbobinsu, domin zirga-zirgar nan tana hana dabbobinsu takiba da samun madara mai yawa.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya