✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Aradu a maimakon Ramadinka! Wani Bafulatni ne yana da wata saniya da yake matukar so. Kawai sai ya wayi gari ba ta da lafiya, sai…

Aradu a maimakon Ramadinka!

Wani Bafulatni ne yana da wata saniya da yake matukar so. Kawai sai ya wayi gari ba ta da lafiya, sai ya yi wa Allah bakance c ewa idan ta warke zai yi azumi 30. Sai kuwa Allah Ya ba ta lafiya. Sai ya fara azumin har ya yi 29, kawai sai saniyar ta mutu. Sai Dan Fulani ya daga kai sama ya ce “To aradu azumin da na yi a maimakon Ramadan dinka!”

Daga Muhammad Umar Foreber, Gashuwa

07066966657

 

Tsintuwar Bakano

Wani Bakano ne yana tafiya sai ya tsinci Naira dubu a kasa. Sai ga wani mutum ya zo wucewa, sai ya ce masa “Kai ba ni ID-CARD dina ne.” Sai Bakano ya ce “Idan ni bakauye ne ai ba wawa ba ne. Yaya sunanka?” Sai mutumin ya ce sunana Central Bank of Nigeria. Sai Bakano ya ce “Shekararka nawa?” Sai mutumin ya ce “Shekarata 1000.” Sai Bakano ya ce “Eh lallai ID Card dinka ne, karbi abinka… amma ka rika sanya hotonka, don ba hotonka ne ajiki ba, sakarai kawai!”

Daga Ibrahim Rabilu, Zamfara

07064282182

 

Up NEPA!

Wani dan Najeriya ne ya je Ingila ya yi laifi ’yan sanda suka bi shi za su kama shi sai ya shiga wani gidan rawa. Suka rasa yadda za su yi su kama shi. Ashe wani daga cikin ’yan sandan ya taba zama a Najeriya, sai ya  ce, “Kun san yadda za ku yi?” Saura suka ce “A’a.” Ya ce, “A kashe wutar lantarkin gidan rawar.” Sai aka kashe. Bayan kamar minti uku ya ce a kunna, ana kunnawa sai wannan dan Najeriya ya ce, “Up NEPA!” Sai ya ce, “Ga shi can, ku kama shi.

 

Shin wannan kaja ne ta girma haka?

Wani dan kabilar Tibi ne ya je gidan ajiye dabbobin daji ne Jos (Gidan Zoo) sai ya ga jimina, yana ta kallonta ya kura mata ido. Ya rasa gane mece ce har zai fita sai ya hango wani Bafulatani a zaune, sai ya dawo ya ce, “Agwai shin wannan kaja (yana nufin kaza) ne ya girma haka?”

Labarai daga 07086866165