Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Mugabe na kwance a asibitin kasar Singapore tun watan Afrilu – Mnangagwa

Mugabe a wani asibiti a qasar Singapore

Mugabe na kwance a asibitin kasar Singapore tun watan Afrilu – Mnangagwa

Tsohon Shugaban Kasar Zimbabwe, Mista Robert Mugabe yana kwance magashiyan a wani asibiti a kasar Singapore, inda yake jinya tsawon watanni, kamar yadda magajinsa, Shugaba Emmerson Mnangagwa ya sanar da kamfanin Dillancin Labarai na AFP, a farkon makon nan.

Mnangagwa a cikin wata sanarwa ya ce, Mista Robert Mugabe mai shekarA 95 a duniya na jinya ne sakamakon wata cutar da ba a bayyana ba; kuma yana samun sauki.

“Shugaban Kasa na farko, dattijo uban kasarmu, Kwamared Robert Mugabe, na can kwance a wani asibiti a kasar Singapore, inda ake jinyarsa.”

“Ba dai kamar a baya ba, inda Mugabe ke daukar hutun wata guda don jinyar; amma likitocinsa a wannan karon sun bukaci ya ci gaba da zama a asibitin don kula da shi na tsawon lokaci, tun watan Afrilun bana, bayan da ya ziyarci likitocin nasa don duba lafiyarsa da ya saba yi lokaci zuwa lokaci,”  inji Mnangagwa.

Shugaban Kasar, wanda a watan Nuwamban bara, ya bayyana cewa, Mugabe ba ya iya takawa da kafarsa, sakamakon rashin lafiya da tsufa, ya ce ya tura wani ayari ciki har da Babban Sakataren Majalisar Gwamnatinsa, Misheck Sibanda, zuwa Singapore don duba jikin na Mista Mugabe.

“Ina farin cikin sanar da jama’ar kasa cewa, tsohon Shugaban Kasa na can na murmurewa; kuma yanayin jikin ya kyautatu, lura da irin shekarunsa,” inji Mnangagwa.

Ayarin da ya ziyarce shi a asibitin ya ce, ‘yana samun sauki cikin hanzari’ kuma sakamakon yadda yake murmurewar ya sa ‘nan ba da jimawa ba, za a iya sallamar Kwamared Mugabe daga asibitin, zuwa gida’.

A lokacin da gwamnati ta sanar da fitar Mugabe zuwa kasar Singapore a watan Afrilu, domin duba lafiyarsa, ta ce ana sa ran komawarsa gida a tsakiyar watan Mayu.

Cibiyoyin kiwon lafiyar na Zimbabwen dai sun yi matukar tabarbarewa; don haka masu hali ke fita zuwa kasar Afirka ta Kudu ko wasu kasashen don samun magani. Mista Mugabe dai a tsawon mulkinsa, galibi ya kasance yana fita zuwa kasar ta Singapore don samun magani.

Mnangagwa dai ya dare madafun ikon kasar ce a watan Nuwanban 2017, bayan ya samu goyon bayan sojin kasar; inda hakan ya kawo karshen mulkin shekara 37 da Mugabe ya yi a mulki. Sai dai an zabe shi a wani zabe mai cike da ka-ce-na-ce, a watan Yulin bara.

Ya yi alwashin farfado da tattalin arzikin kasar mai tangal-tangal, ta hanyar jawo hankalin masu zuba jari kai-tsaye na kasashen waje; sai dai watanni bayan zabensa, muguwar matsalar tattalin arzikin kasa, ta sake dawowa; inda take cin dunduniyar kasar ciki har da karancin burodi da makamashi tare da katsewar wutar lantarki da ta kai wata 18.