✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mugabe ya garzaya kotu don a dage zaben Zimbabwe

Shugaban kasar Zimbabwe Mista Robert Mugabe ya garzaya kotu yana neman a dage zaben kasar da mako biyu.Shugaba Mugabe ya nemi babban kotun kasar ta…

Shugaban kasar Zimbabwe Mista Robert Mugabe ya garzaya kotu yana neman a dage zaben kasar da mako biyu.
Shugaba Mugabe ya nemi babban kotun kasar ta tura zaben gaba da mako biyu kamar yadda Ministan Shari’a na kasar Mista Patrick Chinamasa ya fadi a shekaranjiya Laraba.
Ministan ya fadi a Harare babban birnin kasar cewa ya mika wa kotun takardar bukatar haka a ranar Talatar da ta gabata yana neman “a dage ranar zaben daga 31 ga Yuli zuwa 14 ga Agustan bana.”
Wannan sanarwa ta zo ne ’yan kawanaki, bayan da shugabannin kasashen kudancin Afirka suka matsa wa Mugabe ya jinkirta zaben domin bayar da karin lokaci don yin sauye-sauyen dimokuradiyya.   
Mugabe ya ce kotun tsarin mulki ce ta tilasta ajiye ranar gudanar da zaben a ranar 31 ga Yuli.
Zaben ne zai fito da magajin shugabannin hadaka da aka hada shekara hudu da suka gabata a matsayin hanyar kawo karshen rikice-rikicen siyasa da aka dauki shekaru ana yi.  
Firayiministan kasar Morgan Tsbanigirai, wani babban mai adawa da Mugabe a dogon lokaci ne ya bukaci a yi sauye-sauyen da – suka hada da ba ’yan jarida ’yanci da hana jami’an tsaro shiga harkokin siyasa tare da tabbatar an tsara harkokin zabe bisa gaskiya kafin a je ga kada kuri’a.
A yayin gabatar da bukatar a gaban kotun, Ministan ya ce, “A lokacin taron kasashen Kudancin Afirka, an umarce ni in gabatar da bukata a gaban wannan kotu mai daraja ta a tura zaben zuwa gaba.”