✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman abubuwa 12 daga jawabin Buhari kan zanga-zangar #EndSARS

Ya rarrashi matasa su daina zanga-zanar ya kuma bayyana matakan da ya dauka na biyan bukatunsu

Bayan shafe tsawon lokaci ana kira kan ya fito ya yi magana kan kalubalen tsaron da zanga-zangar #EndSARS ta jefa Najeriya, Shugaban Buhari ya yi wa ‘yan kasar jawabi a ranar Alhamis.

A cikin jawabin nasa da aka watsa kai tsaye, shugaban ya tabo batutuwa da dama, ciki har da rarrashin  matasan su mayar da wuka cikin kube.

Shugaban ya kuma zayyano wasu daga cikin manufofi da tsare-tsaren gwamnatinsa da ya ce ana yin su ne da nufin inganta rayuwar ’yan kasa.

Ga kadan daga muhimman abubuwan da jawabin nasa ya tabo:

  1. Kowane dan kasa na da ’yancin gudanar da zanga-zanga kamar yadda Kundin Tsarin Mulkinmu ya tanadar, matukar ya yi hakan bisa doron doka ba tare da cutar da kowa ba.
  2. Mun ji, mun auna, sannan mun biya dukkannin bukatu biyar da matasan suka mika; Nan take muka rushe sashen ’yan sanda na SARS sannan za mu ci gaba da yin gyaran fuska da nufin inganta aikin dan sanda gaba daya.
  3. Mutane da dama na ganin saurin daukar matakin da muka yi a matsayin gazawa saboda su cimma bukatarsu.
  4. Na kadu matuka kan yadda mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba suka rasa rayukansu sanadiyyar zanga-zangar.
  5. Babu wata gwamnati a tarihin Najeriya da ta yi yunkuri wajen yaki da taklauci kamar tamu.
  6. Mun umarci Hukumar Kula da Albashin Ma’aikata ta Kasa da ta gaggauta dubawa tare da kara albashin ’yan sanda, da ma sauran jami’an tsaro.
  7. Mun kara albashin malaman makaranta saboda muhimmancin da muke ba ilimi da kuma makomar matasa a matsayinsu na manyan gobe.
  8. Za mu yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da hadin kan Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa da kuma samar da nagartaccen shugabanci.
  9. Kamata ya yi kasashen waje su binciki ainihin abin da ya faru kafin su yanke hukunci ba su dauki matsayi cikin gaggawa ba.
  10. Masu zanga-zanga su kauce wa jefa rayuwarsu cikin hatsari ta hanyar guje wa fadawa tarkon marasa kishin kasa masu son ganin dimokradiyyarmu ta fada cikin garari.
  11. In kira ga matasa kan su kara hakuri su bar kan tituna; kun yi korafi kuma mun ji ku, za kuma mu dau mataki.
  12. Ina kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba tare da ba jami’an tsaro hadin kai da tabbatar da cewa ba su cutar da mutanen da aka dauke su aiki su kare ba.