✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmanci da tasirin aiki tukuru a rayuwa

Assalamu alaikum! Ina yi mana gaisuwa wadda ta dace da al’umma. Allah Ya kara mana ni’imar rayuwa da zaman lafiya a kowane lokaci, amin.  A…

Assalamu alaikum! Ina yi mana gaisuwa wadda ta dace da al’umma. Allah Ya kara mana ni’imar rayuwa da zaman lafiya a kowane lokaci, amin. 

A wannan makon kuma, za mu duba muhimmanci da tasirin aiki tukuru a rayuwar dan Adam. Har kullum riba da nasara na nan ga mutumin da ya yi aiki tukuru a rayuwarsa. Domin kuwa komai ka gani a rayuwar nan, yana da sanadin faruwarsa, kamar kuma yadda babu yadda za a yi ka kama zomo ba tare da ka ci gudu ba. Duk wani abu mai kima da muhimmanci, ba a samunsa a haka nan, watau a bagas, kamar yadda masu iya magana kan ce.

Aiki tukuru ba yana nufin ka dawwama, tun daga fitowar rana zuwa faduwarta kan abu guda ba, a’a, ba haka ake nufi ba. Duk aikin da za ka yi, ka tabbatar ka ba shi isasshen lokacin da ya dace, kuma ka aiwatar da shi da gaske ba tare da kasala ba. Sannan ka tabbatar ka ware lokacin sararawa da lokacin cin abinci da lokacin yin ibada, sannan kuma da lokacin tashi daga aikin nan naka. Aiki tukuru na nufin ka yi adalci tsakaninka da aikin kansa da kuma yin adalci ga kai kanka da jikinka, sannan kuma ka yi wa wanda ya sanya ka aikin adalci. Da ikon Allah, za ka samu biyan bukata daidai gwargwado.

Gaskiya da rikon amana, abin dubawa ne wajen gudanar da aikinka ko sana’arka. Su ma wadannan sinadarai ne na sirrin samun nasarar aiki ko sana’a. Sai dai dole mutum sai ya dode kunnuwansa daga surutan mutane, domin a wannan zamani, duk wanda ya ce zai mayar da hankali kacokan ga aikinsa bisa gaskiya da adalci, zai zama wani bako a wurin aikin nasa, domin za a rika kiransa da wasu sunaye na shagube. Za ka ji ana cewa ‘ina ruwan agogo sarkin aiki!’ Ko kuma a rika ce masa ‘Gadu mai aikin banza!’ Ko kuma saboda tsare ka’idar lokaci da ba komai da kowa hakkinsa, sai ka ji ana ce masa ‘wane bai waye ba.’

Irin wadannan maganganu, kada ka yarda su karya maka gwiwa, kada ka amince su maido da kai baya. Duk abin da za ka yi, ka tabbatar kana da yakinin yinsa a zuciyarka, ka tabbatar bisa dokar aiki yake. Idan ka yi haka, komai daren dadewa, kai ne kan nasara, kuma za ka gane amfanin tsare aikin naka, za ka ga ranarsa, wata rana. Domin kuwa duk abin da ka bauta masa, sai ka ci gajiyarsa. Duk abin da ka sadaukar da lokacinka da karfinka da tunaninka wajen aiwatar da shi, to babu shakka ba zai fadi kasa a banza ba. Za ka samu sakamakonsa, komai tsawon lokaci.

Wannan al’amari, kamar yadda misalai suka gabata, mujarrabi ne. Idan ba ka amince ba sosai, tsaya tsaf da ranka ka natsu. Dubi tarihin wani magabaci da kake ganin ya ci nasarar rayuwa, ko kuma ya kai kololuwar nasarar aikinsa ko kasuwancisa. Yi masa tambaya cikin kwanciyar rai, ka ji irin surkukin dajin wahalar da ya ratsa kafin ya kai ga wannan matsayi. Na tabbata idan dai ya ba ka labarinsa tiryan-tiryan, za ka iske cewa ba haka nan ya samu nasarar ba. Ba yana zaune haka siddan aka ba shi nasarar ba. Don haka, raggo dai ba ya suna, kuma duk wanda bai tsaga ba, ba zai ga jini ba, wanda duk bai gina rijiya ba, ba zai samu ruwa ba.

Don haka, kai dai maida hankali ga aikinka, komai kankantarsa, komai rashin ingancinsa, ka yi amanna, sannan ka ci gabadaaiwatar da shi. Babban burinka da farin cikinka na nan tafe wata rana. Babu mamaki ba za ka zama gagarabadau ba a fagen naka, amma dai za ka iya kawo canji na alheri ta wanan aiki naka. Watakila ba za ka iya zama farin wata gama duniya ba, amma kana iya zama wata karamar tauraruwa mai haska ma wasu hanya, a rayuwarsu. Domin a rayuwar nan tamu, ba a taru aka zama daya ba. Zama ne na ’yan marina, kowa da inda ya sanya gabansa. 

Babban darasinmu na yau shi ne, kada mu karaya, mu jajirce mu yi aiki tukuru, bisa amana da adalci da gaskiya. Allah Ya taimaka mana, amin. Sai kuma mako na gaba idan Allah Ya kai mu. Wassalam!