✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmanci da tasirin sabuwar shekara ga al’umma

  A cikin makon nan ne muka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1439 (Bayan Hijira), don haka muke taya dimbin masu karatunmu barka da shiga…

 

A cikin makon nan ne muka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1439 (Bayan Hijira), don haka muke taya dimbin masu karatunmu barka da shiga wannan sabuwar shekara lafiya. Wannan ya nuna mana cewa, rayuwa na nufin shudewa daga wani zango zuwa waccan, domin kuwa watanni goma sha biyu da suka gabata sun yi mana ishara da haka. Wannan dalili ne ma ya sanya muka ga ya dace mu yi tariya da tsokaci game da taken maudu’inmu na yau da ke sama, wato game da rayuwar al’umma, musamman ma sinadaran da al’umma ke bukata domin tunkarar kalubalen da wannan shekara ta bijiro mana da su a rayuwa.

Babu shakka, mutum bai yi kabba ba, bai yi katobara ba kuma bai kwafsa ba, idan ya dauki wannan maudu’in na yau da ke sama, sannan ya nazarce shi da idon basira. Wannan zai ba mutum damar daura babbar damarar tunkarar al’amuran rayuwa gadan-gadan. To, amma idan muka dubi kanun maudu’inmu na yau, mun ambaci al’umma gaba daya, sai dai kuma za mu fi karkata akala ga matasa. Ko me ya sanya? Ga dalili:

Matasa ne aka yi ittifakin sun fi kowa yawa a yanayin rayuwarmu ta yau, kuma su ne mafiya muhimmanci wajen fuskantar rayuwa, haka kuma su ne mafi akasari suke yin nadama da da-na-sanin daukar wani mataki na rayuwa. Matasa ne kan fuskanci babban kalubalen da ke sanyawa ko dai su samu nasara ko kuma su fadi warwas. Dalili ke nan ya sanya za mu yi amfani da wannan lokacin, domin zizara musu wani dan sinadari na rayuwa, domin mu kara masu kaimi, domin mu tada su daga barci, idan barcin suke yi.

A lokacin da muka shiga wannan sabuwar shekara ta Hijiriyya, akwai bukatar matasa su tsaya da ransu, su natsu, su gane muhimmancin lokaci, su daina bata lokaci wajen gudanar da wasu ayyuka ko al’amura marasa tasiri, wanda yin haka babu abin da zai amfane su da shi sai asarar lokacinsu. Ga masu hikimar magana kuwa, sun ce lokaci dukiya ne, duk wanda ya bata shi, ya bata rayuwa.

Idan mun lura da yadda matasanmu suka shantake kuma suke bata lokacinsu wajen gudanar da wasu abubuwa marasa tasiri ga rayuwa, lallai kuwa akwai bukatar a yi musu tambihi, domin ankarar da su, su bi turbar da ta dace.

Ta wace hanya ce matasa za su ci gajiyar lokacinsu a cikin wannan shekara ta Hijiriyya da Allah cikin ikonSa muka shigo? Na farko dai, kamar yadda muka sha nanatawa a wannan fili, yana da kyau mutum ya raba lokacinsa zuwa gida-gida kuma daki-daki, sannan ya aiwatar da al’amuransa bisa jagorancin tsarin da ya yi wa lokacin nasa. Misali, a wannan zamanin, babu abin da ya kamaci matashi kamar neman ilimi. To, kuma ba neman ilimi ne kadai rayuwa ba, don haka sai matashi ya tsara lokacin karatu da lokacin neman wasu abebadai na rayuwa daban.

A nan ne ma ya kamata in jawo hankalin matasa, musamman ma masu bata lokacinsu wajen kallon kwallon Turawa, wanda illar haka har ta yi tasiri a rayuwarsu. Haka na haddasa rugujewar al’amuran matasa da dama. Misali, a wajen kallon kwallon nan, matasa kan shiga lokacinsu na hutu da ma lokacin da za su tsinana wa kawunansu wani aiki na amfani. A wajen kallon kwallon nan, za ka ji ana gardama, wacce ba ta da sidi balle sadada.

kwarai kuwa! Babu dalilin da zai sa matashi ya jajirce yana gardama game da wani mutum, wanda bai san ma shi matashin yana cikin duniya ba. Haka kuma, gardamar ba ta da amfani, domin ba wata karuwa ta ilimi ko dukiya da mutum zai samu a sanadiyyar ta ba. To, me ya yi zafi da mutum zai bata lokacinsa haka?

Wani lokaci ma, illar ba a gardamar kadai take tsayawa ba, abin na yin zurfi har ya kai ga fada. Fada ba karami ba kuwa, domin takan kai ga yi wa juna rauni, wani lokaci ma har da rasa rayuka. To, idan aka yi rashin dacen haka ta faru, mene ne amfanin wannan kallon, kuma mene ne matashin ya samu a sanadiyyar haka?

A lokacin da muka shiga sabuwar shekara, matasa su maida hankali ga ayyukan ci gaba, su guji zaman kashe wando ko zaman maula. Babu abin da mutum zai amfana daga haka sai asara bisa asara. Kuma ina amfanin matashi ya wayi gari bai da abin yi sai dai zaman tsegumi da maula? Mu tuna da cewa, wanda ya mike ya nemi sana’a komai kankantarta, kuma idan dai za ta rufa masa asiri, ya fi ya zauna dashasha, wai sai wani ya nemo, sannan shi ya je yana make murya don a ba shi. Babu shakka wannan ba karamar illa ba ce ga rayuwa. Don haka, muddin matashi ya shiga sabuwar shekara da irin wannan kudurin, na cewa sai an ba shi na zaman kashe wando, to, lallai haka watannin nan goma sha biyu za su shude, ba tare da ya tsinana wa kansa komai ba.

Lallai kam akwai bukatar matasa su dauki babban darasi daga na gaba da su, musamman tsofaffi da ke raye da wadanda suka shude. Tasirin haka shi ne, domin masu iya magana sun ce, da na gaba akan gane zurfin ruwa. Duk wanda ya samu nasarar rayuwa ta fannin ilimi ko dukiya ko kuma rufin asirin rayuwa, akwai dalilin kasancewarsa haka. Domin kuwa a lokacin da yake kuruciya, babu shakka bai wulakanta kansa da lokacinsa ba. Ke nan ya yi amfani da lokacinsa yadda ya dace, wajen neman sana’arsa ko aiki; wanda haka ya sanya ya samu nasarar abin da ya sanya a gaba. A takaice, darasinmu na yau na kira ne ga al’umma, musamman matasa, su fahimta da amfanin lokaci a rayuwa. Su binciki ayyukansu da rayuwarsu na shekarar da ta wuce, sannan su yi nazarin turbar da za su bi a cikin wannan sabuwar shekarar, da nufin samun nasara a rayuwa. Allah Ya taimaka mana, Ya yi mana jagora a cikin wannan sabuwar shekara, amin.