✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmancin gane kayan kwalliya

Mata da dama sukan so su ga sun yi kwalliyar da za ta janyo hankalin jama’a kuma suna son su ga sun fi kowa kyau…

Mata da dama sukan so su ga sun yi kwalliyar da za ta janyo hankalin jama’a kuma suna son su ga sun fi kowa kyau a cikin taro. To, ta yaya hakan zai faru? Hakan zai iya faruwa ne idan an san abubuwa 4 game da kwalliyar zamani wadanda idan aka yi amfani da su, za a ga kyau ya karu.

Sanin launin da ya dace da ido da baki

Babban kuskuren da ake yi idan aka zo shafa kayan kwalliya shi ne, ana shafa launi iri daya a baki da fatar ido. Idan aka yi haka, sai a ga kwalliyar ta yi kama da ta kauyawa. Yadda ya fi dacewa shi ne, a shafa launi daban-daban a fatar ido (eye shadow) sannan a shafa wani launi daban a baki. Misali, idan kayan da aka sanya kore ne, sai a shafa kore a fatar ido sannan a shafa ja a baki. Idan kore ya kasance shi ne a kan ido da baki kwalliyar ba za ta yi armashi ba.

Boye tabo da sanin launin fatarki

Sanin launin da ya dace da fatarki ya fi muhimmanci fiye da komai a kayan kwalliya. Sirrin shi ne, bayan an gama kwalliya za a yi kokarin boye kwalliyar kamar ba a shafa komai a fuskar ba. Idan ana da fuska mai tabo, sai a shafa ‘fondishan’ kafin shafa hoda kuma a tabbata cewa launin hodar fandesho ta yi daidai da launin fata.

Abubuwan da bai kamata a manta ba kafin daukar hoto

A tabbatar cewa an sanya jambaki da hoda domin boye maikon fuska. Kamar kan hanci da goshi da kumatu kafin a dauki hoto. Idan aka yi haka, lallai za a ga an fito daban a hoton.

Abubuwan da za a sanya a jakar kwalliya

Kada a kuskura a bar gida ba tare da an sanya abin goge gumi da jambaki da hoda da turaren jiki da na baki a cikin jaka ba. Kuma kada a manta idan an shiga wajen taro a zama  cikin fara’a kada a rika yamutse fuska. Domin murmushi na kara fitar da kyan mace.