✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmanncin shan ruwa don inganta kwalliya

Ko kun san cewa ruwa na da matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam? Kuma shan ruwa na kara kyau da kuma kwalliya? Domin sai jiki…

Ko kun san cewa ruwa na da matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam? Kuma shan ruwa na kara kyau da kuma kwalliya? Domin sai jiki ya yi kyau sannan idan aka shafa kayan kwalliya, fuska za ta ganu. Don haka ne a yau na kawo muku abubuwa shida da ruwa ke taimakawa wajen inganta kwalliya.

  • Shan ruwa na inganta hasken ido wanda daga an gan ki sai a dauka karamar yarinya ce. Ido babban abu ne wanda ke kara wa mutum kyau sosai don haka idan ido ya yi kyau tabbas in an yi kwalliya, za a burge.
  • Sannan yawan shan ruwa na wanke maikon da ke cikin jiki mutum wanda ke haifar da kuraje da dama. Shan ruwa na sanya fata sulbi da santsi da kuma laushi.
  • Shan ruwa na taimakawa wajen magudanar jini a gangar jiki. Idan magudanar jini na tafiya tsaf ba wata matsala, dole ne a samu lafiya a jiki. Kuma idan jiki ba lafiya, zai wuya a samu lokacin yin kwalliya. Don haka sai a dage da shan ruwa.
  • Yawan shan ruwa na rage fitowar cututtuka da dama daga jiki kamar su kyasbi da kuraje da gautsin fata. Idan aka dage da shan ruwa zai yi wuya a ga wadannan cututtuka sun bayyana a jiki.
  • Shan ruwa na sanya kwazo a wajen aiki sannan yana taimakawa wajen samun barci mai dadi ba tare da yawan farkawa ba. A dage da shan ruwa domin samun kwanciyar hankali domin, sai hankali ya kwanta kafin a samu lokacin yin kwalliya. Yana da kyau akalla a sha kofi daya da safe da rana da kuma dare a duk lokacin da za a ci abinci.
  • Ruwa na taimakawa wajen korar cututtuka domin idan ana yawan shan ruwa za a yawaita zuwa ban-daki yin haka kuma na wanke cututtukan mara da sauransu. Yana kuma kara taimaka wa zuciya aika jini a sauran magudanun jini ba tare da samun wata matsala ba.