✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mukarraban Gwamnatin Wamakko sun koma Jam’iyyar APC

Mukarraban gwamnatin Aliyu Magatakarda Wamakko da suka hada da kwamishinoni da sauran ’yan Majalisar Zartarwar Jihar da shugabannin kananan hukumomi 23 da masu ba da…

Mukarraban gwamnatin Aliyu Magatakarda Wamakko da suka hada da kwamishinoni da sauran ’yan Majalisar Zartarwar Jihar da shugabannin kananan hukumomi 23 da masu ba da shawara da shugabannin Jam’iyyar PDP sun canja sheka zuwa Jam’iyyar APC a ranar Litinin da ta gabata.
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Alhaji danladi Bako ne ya bayyana canja shekar a madadin gwamnatin jihar, “bayan dogon nazari da tuntubar juna da mukayi kan siyasar kasar nan da kuma ci gaban jihar nan, mun yanke shawarar komawa Jam’iyyar APC. Wannan hukunci mun yanke shi ne bisa ga yardar Sakkwatawa kan kasawar Gwamnatin Tarayya ta kawo cibgaba a jiharmu” inji Kwamishina Bako.
Shugaban karamar Hukumar Sabon Birni Alhaji Idris Muhammad Gobir wanda ya yi magana a madadin shugabannin kananan hukumomi jihar ya ce, “Muna tare da mai girma Gwamna duk inda ya je ba gudu ba ja da baya, ba yadda za a yi mu ci gaba da zama a wannna jam’iyya ta PDP.”
 Tsohon Sakataren Jam’iyyar PDP na Jihar Alhaji Aminu Bello ACY ne ya yi magana a madadin shugabannin jam’iyyar, inda ya bayyana ficewarsu daga cikinta tare da komawa APC.
Alhaji Aminu Hassan Shagari Mai ba gwamna shawara kan gajiyayyyu ya yi magana a madadin abokan aikinsa, inda ya ce “ba mu gamsu da Jam’iyyar PDP ba.”
Sai dai Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Muktari Shehu Shagari ya ce shi yana nan a jam’iyyarsa ta PDP bai bar ta ba, kuma bai yi shirin bari ba. “Ina nan cikin jam’iyyata, katina da na karba na dan jam’iyya tun 1999 ban canja shi ba har yanzu ni dan PDP ne, wannan shiri na canja sheka ban san da shi ba sai yau, domin ba wanda ya tuntube ni a kai balle na je wurin, magoya bayana mu yanke shawara kan haka, ni ban canja jam’iyya ba,” inji Mataimakin Gwamnan.