✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mulatu: Jakadan Habasha a Turkiyya ya zama shugaban kasa

Majalisar kasar Habasha ta zabi Mulatu Teshome a matsayin shugaban kasa na tsawon wa’adin shekara shida a kan mulki. A wani zaman da aka yi…

Majalisar kasar Habasha ta zabi Mulatu Teshome a matsayin shugaban kasa na tsawon wa’adin shekara shida a kan mulki. A wani zaman da aka yi tsakanin ’yan majalisar wakilai da dattijai, an amince da zaben Jakada Dokta Mulatu Teshome a matsayin shugaban kasar Habasha,” kamar yadda Ma’aiaktar Harkokin Wajen kasar ta bayar da sanarwa
karfin ikon mulkin kasar ya rataya ne a kan Firayiminista Hailemariam Desalegn. Shi kuwa Mulatu dan shekara 57, wanda a da jakadan Turkiyya ne kafin nadinsa, ya maye gurbin tsohon shugaban kasar, Girma Wolde Giorgis, dan shekara 88, wand aya fara hawa karagar mulki a shekarar 2001, sannan aka sake zabensa a shekarar 2007.
“Ina jin cewa an karrama ni, idan aka zabeni a amtsayin shugaban kasa Tarayyar Dimokuradiyyar Jamhuriyar Habasha,” a cewar Mulatu, bayan da aka rantsar da shi, don kama ragamar mulki, sannan ya yi alkawarin aiwatar da tsare-tsaren bunkasa kasa. Mulatu dan kabila mafi yawan al’umma ne a kasar Habasha, wato Oromo ya yi aikin difulomasiya a kasashe da dama, inda ya taba zama jakadan kasashen Sin da Japan da Turkiyya; sannan ya taba rike mukamin ministan harkokin noma.
Shi ma Firayiminista Hailemariam Desalegn ya kama ragamar mulki ne, bayan da aka rantsar da shi a bara, wata daya bayan mutuwar Meles Zenawi.