✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mulkin gaba da kama-karya ne matsalarmu – Saminu Turaki

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Ibrahim Saminu Turaki ya ce a kasar ne kawai shugabanni suke mulkin gaba da kama-karya, saboda sai mutum yana kan…

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Ibrahim Saminu Turaki ya ce a kasar ne kawai shugabanni suke mulkin gaba da kama-karya, saboda sai mutum yana kan mulki yake da daraja ake ganinsa da kima.
Alhaji Ibarhim Saminu Turaki ya bayyana haka ne a garin Kazaure lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Asabar da ta gabata jim kadan da yin gangamin Saminiyya da ya gabatar a gonarsa da ke hanyar ’Yankwashi.
Ya ce “A Najeriya ne wanda ya gaje ka ba ya ganin girmanka sai ma ya ce zai yi amfani da babban joji ko Kwamashinan ’Yan sanda ya ci maka mutunci saboda shi ne Gwamna. Masu irin wannan hali kamar yadda suka binciki shugabannin baya, su rubuta su ajiye haka za a yi musu bincike domin haka ne tsarin kasar, haka muka iya.”
Sanata Turaki ya ce matsalar da mutanen Arewa suke fuskanta suke ganin kamar matsala ce daga mutanen Kudu ba haka ba ne, “Matsalarmu tana karkashinmu, mu ne ba ma son kanmu da kanmu domin mu ne ake amfani da mu muke ci wa ’yan uwanmu dunduniya mu ke bata su domin biyan bukatun kanmu,” inji shi.
Ya ce duk tinkahon da Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido yake yi yana hura hanci “yanayi ne da bazata, domin Lamido bai taba cin zabe ba sai da ya shigo inuwata aka zabe shi domin Jam’iyyar PDP ba ta taba cin zabe a Jihar Jigawa ba sai da na shiga cikinta na tsayar da shi ya ci zabe,” inji Turaki.
Game da kowace jam’iyya ya shiga, ya ce yana kungiyar Saminiya Amana ne kuma yana samun goyon bayan ’ya’yan Jam’iyyar APC da na PDP, amma har yanzu bai yanke hukuncin jam’iyyar da zai fada ba sai nan gaba.