✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mulkin Najeriya ya fi karfin Lamido – Matasan APC

Matasan Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa sun nuna damuwa kan yadda talauci da rashin aiki ya yi wa mutanen jihar katutu, duk da irin ayyukan…

Matasan Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa sun nuna damuwa kan yadda talauci da rashin aiki ya yi wa mutanen jihar katutu, duk da irin ayyukan da gwamnatin jihar take ta kwakwazo ta yi wa jama’a a daukacin kananan hukumominta 27 a cikin shekara shida na gwamnatin Lamido.Saboda haka Lamido ba zai iya rike Najeriya ba.
Shugaban Matasan Jam’iyyar APC a Jihar, Malam Nazifi Salisu ya bayyana haka a Dutse a wani taro da suka yi da manema labarai a harabar gidan Rediyon Freedom a ranar Litinin da ta gabata.
Ya ce ba za su sake sakaci a ce sun bar jam’iyya mai ci ta sake kafa gwamnati a Jihar jigawa ba, kasancewar babu abinda gwamnatin Lamido ta yi wa talakawan jihar ta fannin gina al’umma sai gine-gine marasa ma’ana da suke cike da beraye da kadangaru.
Ya ce daga yanzu an daina amfani da matasa wajen shirya magudin zabe kuma za su tsaya tsayin daka wajan ganin an bi doka an wanzar da zabe na gaskiya a fadin jihar, “Sakamakon haka ne ma ya sa muka ga ya dace mu shiga birni da kauye don wayar wa matasa kai kan illar magudin zabe,” inji shi.
Ya ce ayyukan raya kasa da gwamnatin jihar take ikirarin tana yi wa al’umma ba a ko’ina take yi ba, tana yi ne a wasu wurare da ta kebe domin in aka dauke hedkwatar jihar da na wasu kananan hukumomi ba inda ake yin ayyukan, ya ce wata hedkwatar karamar hukumar ba ta da bambanci da rugar Fulani. “Amma mutanen karkara har yanzu ba su san akwai gwamnati a Jihar Jigawa ba domin in ka dubi rayuwarsu babu wani kayan more rayuwa da za su nuna su ce gwamnati ce ta yi musu saboda ta san da zamansu.