Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mummunan halin da kasarmu take ciki

Ko shakka babu gwamnati ita ce uwa kuma makarbiya a kan duk wata tashin-tashinar da ke addabar al’umma saboda masu rike da ita su ne jagorori kuma sun yi rantsuwa za su tsare rayuka da dukiyoyin mutane. Amma an ce in an bi ta barawo abi ta mabi sawu. Akwai gudunmawar da jama’a za su ba da ta hanyar taimaka wa jami’an tsaro don tona masu wannan aika-aika gami da sanya karfe da dabarun da Allah Ya ba su don hada karfi da karfe.

Sai babbar gudunmawa ta hanyar komawa ga Allah da barin aikata miyagun ayyuka wadanda su kadai suna iya sanya Allah Ya darkake kowace irin al’umma, kamar ayyukan asiri da zubar da jinin wanda ba su ji ba su gani ba da kashe jarirai tun a ciki da sauransu.

ADVERTISEMENT

Allah Madaukakin Sarki Yana fada a cikin Suratul Bakara “Tabbas za a jarraba ku da wani abu na daga tsoro da yunwa da tawaya ta dukiya da rayuwa da kayan marmari, amma a yi wa masu hakuri bushara. Su ne wadanda in masifa ta same su za su ce daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma.”

Da na zauna na kalli wannan ayar ga ta ba yau aka saukar da ita ba kuma sai ya kasance kamar yanzu aka saukar da ita kuma a kan ’yan Najeriya.

ADVERTISEMENT

Dama kamar yadda muka sani shi Alkur’ani ya dace da jiya da yau da ma gobe kuma ya sauka ga Shugaban Halitta, kamar yadda Allah Madaukaki Ya fada. Abin lura a cikin wannan ayar Allah Ya lissafo wasu abubuwa kamar haka;

  1. Tsoro (rashin tsaro)
  2. Yunwa (tsadar abinci)
  3. Talauci
  4. Rasa rayuka.

Kusan halin da muke ciki ke nan amma daga karshe sai Allah Ya ce: “A yi wa masu hakuri bushara.”

Ke nan da za mu hakura da wannan jarrabawa da Allah Yake yi mana tunda Shi Ya fada, ko shakka babu akwai wata garabasa da Allah Ya yi mana tanadi kuma a karshen ayar Ya ce “Wadancan su ne shiryayyu.”

Duk karshen lamarin in muka hakura Aljanna ce makomarmu. Amma ta yaya za mu yi hakuri har mu rabauta?

  1. Sai mun dauka cewa wani mutum ba ya yin sanadiyar saka ka a wani hali sai dai Allah Ya jarrabe ka don Ya ga karfin imaninka.
  2. Sai mun koma ga Allah mun tuba daga zunubanmu sai Allah Ya saukar mana da rahamarSa da ruwan sama da abinci yalwatacce.
  3. Shugabanni su ji tsoron Allah su kyautata wa al’umma.

Muna rokon Allah Ya fitar da mu daga cikin wannan tsanani da muke ciki na rayuwa, Ya ba shugabanninmu fikira da ikon gudanar da mulkinsu bisa adalci.

 

Sanusi Hashim Abban Sultana daga Jihar Katsina

08065507271