✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun amince da dokar kisa ga masu ga garkuwa da mutane – Ustaz Tahir

Wani malamin Musulunci, Ustaz Tahir Zubairu ya ce sun amince da dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane da wasu gwamnatocin jihohin Arewa suka…

Wani malamin Musulunci, Ustaz Tahir Zubairu ya ce sun amince da dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane da wasu gwamnatocin jihohin Arewa suka fara kafawa. Sai dai ya ce, “Yawan kafa doka ba tare da aiwatar da ita ba yana mayar da hannun agogo baya, tabbatar da yin aiki da irin wadannan dokoki ne zai taimaka wajen samun raguwar aukuwar miyagun ayyuka.”                                                                                                                                              Malamin wanda ya fadi haka cikin zantawa da Aminiya a Ibadan ya ce, “Idan har an kafa irin wadannan dokoki to ya kamata a ce ana aiwatar da su yadda ya kamata domin ya zama izna da wa’azi ga wadanda aka kafa dokar dominsu.”

Ustaz Tahir Zubairu, ya yi kira ga mahukuntan Najeriya su tabbatar da cewa, suna yin aiki da dokokin da suke kafawa domin samun zama lafiya a tsakanin al’ummarsu . Ya ce, “Kamar yadda Allah Ya yi bayani cikin Alkur’ani cewa, idan an kama masu laifi to a yanke musu hukunci a bayyane a gaban jama’a ba a boye ba. Idan ana yin haka to gobe wani ba zai yi sha’awar aikata irin wannan laifi ba.

“Idan ana hukunci kowa yana gani a zahiri to masu sha’awar aikata miyagun ayyuka za su ragu amma hukunci a dukunkune ko a boye shi ne yake sa karuwar miyagun ayyuka a kasa. Wannan shi ne koyawar da Allah  Ya yi mana kuma shi ne zai sa mu samu cin nasara a duk al’umarin da ya shafi tsaron kasa,” inji shi.

Malamin ya ce, “Wannan babbar matsala da manyan mutane suke amfani da matsayinsu wajen hana hukunta ’ya’yansu da aka kama da laifi dumu-dumu tana kawo koma baya ga rayuwarmu baki daya. Allah Ya yi mana bayani a cikin Alkur’ani cewa, idan masu karfi daga cikinsu suka aikata laifi sai a kyale su, ba tare da hukunta su ba, amma sai a hukunta masu rauni daga cikinsu. To matukar ba a daidaita hukunci a tsakanin mai karfi da mai rauni ba, to babu yadda za a iya yin maganin aukuwar miyagun ayyuka. Aiwatar da doka ta fannin zartar da hukunci ga kowa shi ne ya sa wasu kasashen duniya suka yi gaba domin babu zancen kamun kafa ko neman alfarma a wurinsu duk wanda ya aikata laifi ana yi masa hukunci daidai da laifinsa ne.”