Search
Subscribe
Mun amince da hana almajirci da barace- barace

Mun amince da hana almajirci da barace- barace

Salam. Fatan alheri gare ku ma’aikatan Aminiya mai farin jini. Don Allah Edita ka taimaka ka ba ni dama in yi jinjina ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa kafa dokar hana almajirci da barace-barace a Arewacin kasar nan. Tabbas wannan kokari da kishi abu ne mai kyau, domin wannan al’amari yana ci mana tuwo a kwarya, a ce yaranmu na Arewa su ne koma-baya a fagen ilimin zamani da sana’o’in dogaro da kai. Tabbas babu wata kasa da za ta kai bantenta idan har al’ummar kasar sun maida barace-barace sana’arsu. Duk da haka ya kamata shugabanni da mawadatanmu su rika tausayin na kasa, domin Ubangiji Yana tare da bayinSa masu taimakon mabukata. Ubangiji bai rage mu da komai ba na daga arzikin karkashin kasa, amma wadansu tsirarun mutane sun mallaka wa kansu da ‘ya’yansu. Allah Ka gyara mana kasarmu da al’amuranmu.

Daga Murtala Ahmed Abubakar, Kwalli Gidan Doki 07068295953. Daga Tukur Sani Kwasara Karamar Hukuma Bagudo Jihar Kebbi. 08063365514.

Kira ga Hukumar NCC

Assalam. Don Allah Aminiya ku isar min da sakona zuwa ga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), cewa mu mutanen Yobe masu amfani da layukan sadarwa mun gaji da damfarar da ake yi mana, a yi mana maganin wannan damuwar. Sai ka ji wanda ka kira ya ce ba ya jin ka ko dukkanku ba kwa jin juna. Su kuma layukan sadarwa sun riga sun cire maka kudi alhalin ba ka biya bukatarka ba.

Daga Sa’idu Ya’u Damaturu,YBS, 07033279415.

Taki ya fi karfin manomi

Assalam. Haba shugabannin Najeriya tukuicin da za ku yi wa manoma ke nan takin zamani ya fi karfin manomi mai karamin karfi.

Daga Tukur Maraya, Shanono, 07032442923.

Nasarar jam’iyyun adawa a kotu

Ina gaisuwa ga ma’aikatan jaridar Aminiya mai farin jini, kuma muryar talaka. Kotun Kolin Najeriya daminar bana ba irin ta bara ba ce, kwado ya fada a ruwan zafi. Domin yanzu jam’iyyun adawa ke samun nasarar shari’a, ba kamar lokutan baya ba. Hakan kuwa zai dore? To Allah Ya sa ya dore amin!

Daga Suleiman Adam K, 07017846306.

Fatan alheri ga Shugaban yankin Soba

Assalam alaikum, ina yi wa Shugaban Karamar Hukumar Soba da jami’ansa da dukkan masu madafan iko fatan alheri a kokarin da suke yi na sauke nauyin da talakawa suka dora musu. Allah Ya taya ku riko amin.

Daga Isah Murtala Gama-Gira. 08135419744.

Gwamnatin Bauchi a samar  wa matasa aiki

Assalamu alaikum. Edita ina so ka ba ni dama in shawarci sabon Gwamnanmu na Jihar Bauchi, Alhaji Bala Abdulkadir Mohammed Kauran Bauchi kan ya taimake mu yadda Allah Ya taimake shi ya kawo mana ayyukan ci gaba a jiharmu, kuma ya sama wa matasanmu ayyukan yi su bar zaman banza. Allah Ya taimake ka amin summa amin.

Daga Nasir Malami Sidi, Malam Goje, Bauchi, 08036311157.

Ba na goyon bayan raba Masauratar Kano

Assalamu alaikum Edita. Ina sake rokon ka ba ni dama in yi magana a kan kirkiro masarautu a Jihar Kano. Ina ganin wadansu jama’a marasa kishin kasa suna jinjina wa masu kokarin raba masarautar. Wallahi kara masauratu a Jihar Kano ko kadan ci baya ne ci na karshe, ya kawo rage kimar Kano da masauratar baki daya a idon duniya. Mai karatu ba za ka san haka ba sai nan gaba. A matsayina na dan asalin Jihar Kano, ba na goyon bayan raba mana masauratarmu ya kamata gwamnatin Jihar Kano ta gane cewa bakin jini take kara wa kanta a yanzu a idon Kanawa.

Daga Jibril A. Aliyu, Kano, 07034281614

Taya murna ga shugabannin Kasuwar Mil 12

Salamun alaikum Edita. Ina yi muku fatan alheri. Ina so in yi amfani da wannan dama domin nuna farin cikina ga jagoranmu kuma babanmu Alhaji Sa’adu Kaita bisa hadin kai da aka samar a babbar kasuwa ta Afirka wato Kasuwar Mil 12 da ke garin Legas. Shugabanninmu sun hada kawunansu baki daya, Alhaji Sa’adu Kaita da Alhaji Isah da Alhaji Kabiru da Alhaji Haruna Muhammad, Allah Ya kara hada kawunanmu da sauran Musulmin duniya baki daya.

Daga Sa’ad Sa’eed Kiru, Kasuwar Mil 12, Legas, 08062572330.

Allah kara ba jami’an tsaro nasara

Assalam Edita. Muna rokon Allah Ya kara ba jami’an tsaron Najeriya nasara, su kara kama irin su Bawa Na-Gwamma da sauran batagari masu kashe jama’a ba hujja. Ja mu je zuwa Baba Buhari. Allah Ya taimaka maka!

Daga Ibrahim Malami Katsina, 07062903579.

Abin da zai rage wa matasa shaye-shaye

Ina kira ga gwamnatocin jihohi su rika karfafa harkokin wasanni a jihohinsu domin matasanmu su kau ce wa shaye-shaye.

Daga Saminu Mayen Tea, Batsari 08036773485.

Jaje ga gwamnatin Nijar

Salam Edita. Muna jajanta wa gwamnatin Jamhuriyyar Nijar game da kisan dan majalisa da ’yan bindiga suka yi. Allah Ya kiyaye aukuwar hakan nan gaba amin.

Daga Abu Yazyd Loko 07054550669.

Gargadi ga barayin gwamnati

Don Allah Edita ka ba ni dama in yi gargadi ga wadansu ’yan tsirarin mutane wadanda ke sace dukiyar al’umma cewa su ji tsoron Allah. Kada fa su manta cewa a Lahira babu lauya, kuma yadda mutum ya zo a tsirara haka zai koma tsirara.

Daga Abdullahi Ashiru Katsinan Dikko, 08060568380.

Garin Waire na fama da rashin ruwa da wuta

Salam. Muna kira ga Mai girma Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya dubi mazabar Waire da ke Karamar Hukumar Bichi wadda ba ta da hanya ba wutar lantarki kuma babu ruwan famfo. A tausaya mana Mai girma Gwamna.

Daga Alhaji Musa Badawa Waire Bichi, Jihar Kano 08068992280.

Jinjina ga Salihu Dila Kamba

Salam Edita, da fatan kuna lafiya Allah Ya sa haka amin. Don Allah ina son ku ba ni dama in yi jinjina ga Alhaji Salihu Garba Dila Kamba Dogo Baban Tima ciyaman namu. Wallahi mu matasa muna kara yi wa Allah godiya da Ya ba mu ciyaman mai tausayin talakawa sama da shekara 20 ba a taba samun irinsa ba. Allah Ya taya ka riko.

Daga Al-Khairu M. Talibu Kamba 08056109087.

Musulmi da Kirista mu zauna lafiya

Zaman lafiya ya fi komai dadi a duniya. ’Yan kasata Najeriya mu yi karatun ta-natsu mu kauce wa fadace fadacen kabilanci da addini mu rungumi junanmu Musulmi Da Kirista mu zama tsintsiya madaurinki daya.

Daga Alhaji Bilya Doya Boy, Zauro Jihar Kebbi 07067467444.

Hajji da man fetur: Kira ga Shugaba Buhari

Assalamu alaikum Edita. Ina kira zuwa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya dubi girman Allah Wanda Ya halicce mu kuma Ya damka masa mulkin Najeriya Ya maida tallafin kudin aikin Hajji da tallafin man fetur. Da fatan kirana zai isa gare ka.

Daga Abdullahi Lawali, Abul Aiman, Jihar Zamfara, 07037001720.

Fatan alheri ga gwamnatin Zamfara

Ina taya Zamfarawa murnar hukuncin Kotun Koli. Allah Ya sa Matawalle ya yi muku adalci ya kawo muku tsaro da hanyoyin samun saukin rayuwa. Allah Ya kiyashe ku maimaita irin mulkin baya. Mun gode wa Allah.

Daga Jamilu M. Adam 08036883363.

Kira ga Hukumar EFCC

Assalam Editan Aminiya. Don Allah ga sakona zuwa ga Hukumar EFCC don Allah ta ziyarci Ma’aikatar Gona ta Tarayya a Abuja.

Daga 08028994837, Abuja.

Kira ga Gwamnatin Kebbi

Salam Edita. Ka ba ni dama in yi kira ga gwamnatin Jihar Kebbi, kan ta taimaka a kawo mana Netwok na MTN ko Glo ko Airtel a Aljannare Karamar Hukumar Dakingari Jihar Kebbi.

Daga Idris Yaro, Abuja 08028994837.

Buhari talakawa na yi maka kyakkyawan zato

Assalam. Shugaba Buhari don Allah ya tuna fa lokacin zabe, ba jam’iyya aka yi ba shi aka yi ’ya’yan kowace jam’iyya kai suka zaba, saboda haka kowa naka ne domin ana yi maka kyakkyawan zato ka dubi talakawanka a halin da suke ciki don Allah.

Daga Shamsuddeen Mukhtar, Dansarai, Gezawa, Jihar Kano, 08038074021.

Hajiya Khurera ce mai kamar maza

Assalam Aminiya. Ina mika dimbin gaisuwa zuwa gare ku. Kuma ina mika jinjinata ga Hajiya Khurera, mace mai kamar maza, ban taba jin labarin da ya birge ni ba irin wannan, ina yi miki fatan alheri.

Daga Sa’adatu Gumel, Jihar Jigawa 07037127278.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin