✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun bar iyalanmu a Afirka ta Kudu- ‘Yan Najeriya da suka dawo

Wasu ‘Yan Najeriya da aka dawo da su gida daga kasar Afirka ta Kudu sakamakon rikicin kin jinin baki da ‘yan kasar ke nuna wa…

Wasu ‘Yan Najeriya da aka dawo da su gida daga kasar Afirka ta Kudu sakamakon rikicin kin jinin baki da ‘yan kasar ke nuna wa ‘yan kasashen waje, sun bayyana cewa sun dawo Najeriya ba tare da wani abu a hannun su ba.

Wani dan asalin jihar Ondo mai suna Segun Salau mai shekara 32 da ya kai shekara biyar yana kasar Afirka ta Kudu. Ya bayyanawa Aminiya cewa, zamansa a Afirka ta Kudu ya kasance ako da yaushe yana cikin fargaba saboda harin da ake kaiwa baki a kasar, a wannan harin da aka kaiwa ‘yan Najeriya an shiga shagon ‘yar uwata inda aka lalata mata kayan shagon tare da yi mata asarar dukiyarta.

“Ba ni da wani dalilin koma wa nan gaba Afirka ta Kudu saboda sau uku kenan ina ganin abin da ake yi wa baki a kasar.” Cewar Segun.