✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun ga tasku a hannun masu garkuwa da mu – Ahmad Sulaiman

Da jijjifin shekaranjiya Laraba ce sojojin Birged na 17 da sauran jami’an tsaro suka yi nasarar kwato sanannen Malamin nan Alaramma Ahmad Suleiman da mutum…

Da jijjifin shekaranjiya Laraba ce sojojin Birged na 17 da sauran jami’an tsaro suka yi nasarar kwato sanannen Malamin nan Alaramma Ahmad Suleiman da mutum biyar da suke tare da shi da masu garkuwa da mutane suka sace a ranar 14 ga Maris din nan a hanyar Sheme Kakumi zuwa Kankanra.

Alaramma Ahmad Sulaiman suna hanyarsu ta dawo ne daga Jihar Kebbi bayan sun halarci wani wa’azi, inda masu garkuwa da mutane suka sace su.

Sace malamin wanda daya ne daga cikin malaman Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, ta jawo cece-kuce musammaan a kafofin sadarwa na zamani ta Facebook da sauransu.

Da yake jawabi a wajen mika malamin ga fadar Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir wanda Kauran Katsina ya wakilta, Kwamandan Birged na 17 da ke Katsina, Birgediya Janar Lukman T. Omoniyi ya ce, sojoji da takwarorinsu jami’an tsaro sun yi nasarar ceto malamin da sauran mutanen ne bisa umarnin Babban Hafsan Sojojin Kasa Laftana Janar Tukur Burtai.

Birgediya Janar Omoniyi ya ce rahoton sirri da suka samu da kuma hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro sun taimaka musu wajen kai farmakin da suka yi nasarar ceto malamin da sauran mutanen.

Kwamandan ya tabbatar wa jama’a cewa jami’ansu za su ci gaba da aikin don ganin ana samun cikakken tsaro a jihar.

A  jawabin Alaramma Ahmad Suleiman ya bayyana irin zaman kunci da wahalhalu da tasku da suka fuskanta a lokacin da suke hannun masu garkuwa da su.  Malamin ya ce,”Kullum abin da suke ce mana shi ne, tunda an hana su komawa daji, kuma hukuma ta shigo cikin batun to ko an kawo kudin fansa kashe mu za su yi. Kullum wannan kalma ita muke ji daga wajensu, sannan sai su zo a gabanmu su rika harbe-harben bindiga.”

Malamin ya kara da cewa, kwanakin da suka yi a hannun masu garkuwa da mutanen kwanaki ne masu wahala matuka. “A wasu lokutan ni ke ba yaran hakuri idan suna kuka, yayin da wani lokacin yaran ne za su rika ba ni hakurin ni ma in ina kuka. A wasu lokutan suna hana mana abinci da ruwa,” inji shi.

Malamin ya roki Allah cewa ko da wani laifi muke yi to Allah Ya yafe mana.

Ya yi godiya ga Allah da sauran jama’a bisa ga addu’o’in da aka rika yi musu.

Ita kuwa Masarautar Katsina jinjinawa ta yi kan wannan namijin kokari da jami’an tsaro suka yi na ceto wadannan mutane. Sannan ta ce, za ta c igaba da bayar da tata gudunmawar a wajen ganin an samu tsaron, inda ta sake yin kira ga hakimai da magaddai da masu unguwanni su kara zuba ido gami da kawo rahoton duk wani abu da ba su aminta da shi ba.

Masarautar har ila yau, ta yi kira ga sauran jama’a su kara bayar da muhimmanci a kan abin da ya shafi tsaro a tsakaninsu.

Shi kuwa fitcacen malamin nan kuma jigo a Kungiyar Izala, Sheikh Yakubu Musan Hassan bayan ya yi godiya ga Allah ya kuma yi godiya ga jami’an tsaron bisa yadda suka ceto wannan malami da sauran malaman da aka yi garkuwar da su, ya ce “An ceto Malam ba tare da an bayar da ko Kwabo ba.”

Sheikh Yakubu Musa Hassan ya bayyana haka ne ga manema labarai dangane da batun ceto malamin da jami’an tsaron suka yi a Katsina.

Tun a shekaranjiya Laraba Alaramma Ahmad Sulaiman da abokan tafiyarsa suka koma ga iyalansu, bayan da suka shafe kwana 13 a hannun masu garkuwa da mutanen.

Wani na kusa da malamin, Malam Muhammad Kabir ya bayyana wa Aminiya a Kano cewa malamin yana nan cikin koshin lafiya. “A yanzu haka malamin ya dawo cikin iyalinsa, muna yi ga Allah godiya bisa yadda Ya tserar da malamin daga hannun masu garkuwa da shi,” inji shi.