✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun gamsu da salon magance matsalar tsaron Jihar Zamfara  – Sani Aiki Maikyau

An bayyana kalubalen tsaro da ya addabi jihohin Arewa maso Yamma musamman Jihar Zamfara da cewa al’amari ne da ya wuce musaltuwa kuma  kai taron …

An bayyana kalubalen tsaro da ya addabi jihohin Arewa maso Yamma musamman Jihar Zamfara da cewa al’amari ne da ya wuce musaltuwa kuma  kai taron  tattauna matsalar tsaro da Gwamnan Kabiru Matawalle ya yi  zuwa Dubai a Hadaddiyar Daular  Larabawa abu ne da ya dace.                                                                                                                                                     Wani dan asalin Jihar Zamfara Alhaji Sani Bala Aiki Maikyau ne ya bayyana haka a zantawarsa da Aminiya a Kalaba, inda ya ce, “Tsofaffin shugabannin jihar sun kasa shawo kan matsalar har abin ya ta’azzara kuma alhakin gwamnonin jihar na yanzu da na baya ne su magance matsalar tare da sauran shugabannin jihar.”

Game da zargin wadansu sarakuna da sakaci ko hannu a matsalar tsaro da ta satar shanu ya ce, “Gaskiya abu ne wanda ke boye, Allah kadai ne Ya san abin da ke tsakanin al’umma amma yana da alaka da hakan saboda yawanci wasu abubuwan na faruwa yankunan su ba su iya magana.”

Alhaji Bala Aiki Maikyau ya ce, “Kai taron duba matsalar tsaron jihar zuwa Dubai da Gwamna Matawalle ya yi, ya kyauta. Dalilina na fadin haka shi ne mafi alheri da zai kawo mana masalaha ta zaman lafiya a jiharmu Ubangiji Allah Ya ba shi nasara.” Ya ce, ya goyi bayan kai taro tsaron zuwa Dubai ne domin an rika samun matsaloli a shugabannin baya ta yadda da an zauna taron sirri irin wannan kafin a ce wani abu sirrin ya bayyana a kunnen wadanda ba a so su ji ko su sani. Shi ya sanya ya yanke shawarar kauce wa yin kitso da kwarkwata ya kai taron can.

Alhaji Sani Bala Aiki Maikyau, ya shawarci Gwamnan Jihar Zamfara ya kula da sauran al’umma da daliban da suka kammala jami’o’i da manyan  makarantu da suke zaune babu aikin yi, inda ya ce idan aka ba su aikin yi hakan zai rage wasu matsalolin da jihar ke fuskanta.