Aminiya

Mun gamsu da  ziyarar Osinbajo a Kudu maso Yamma – Shugabannin Fulani

Alhaji Yakubu Bello Shugaban Qungiyar na Jihar Oyo.

Shugabannin Kungiyar Miyetti Allah a Kudu maso Yamma sun yaba da matakin  da Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo da Shugaba Muhammadu Buhari ya umarta ya dauka domin tattauna matsalar tsaro a tsakaninsa da manyan sarakuna da masu ruwa-da-tsaki a sashen.

A ranar Asabar da ta gabata ne Farfesa Osinbajo, ya fara isar da sakon Shugaba Buhari ga Awujale na Ijebu, Oba Kayode Sikiru Adetona da Akarigbo na Remo Oba Babatunde Ajayi duk a Jihar Ogun, inda ya yi ganawar sirri da sarakunan kan tabarbarewar tsaro. A kan haka ne Aminiya ta zanta da shugabannin Kungiyar Miyetti Allah na jihohin Ondo da Oyo da Ekiti wadanda suka yi maraba da wannan mataki da Shugaba Buhari ya dauka tare da bayar da shawarwari ga mahukunta da dukkan al’ummar Najeriya.

ADVERTISEMENT

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na Jihar Oyo Alhaji Yakubu Bello cewa, ya yi “Shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci yabo  kan daukar matakin gaggawa dangane da kalaman barazanar raba kasa da ke fitowa daga bakin wadansu shugabannin Yarbawa da kungiyoyinsu. Mun yi tir da Allah wadai da kisan gillar da wadansu ’yan bindiga suka yi wa Funke Olakunri ’yar Shugaban Kungiyar  Yarbawa ta Afenifere kuma muna rokon Allah Ya tona asirin wadanda suka aikata wannan mummunan aiki da ya haifar da jita-jitar da ake danganta aukuwar lamarin da Fulani makiyaya.”

“Kamata ya yi al’ummomi da kabilun kasar nan mu yi aikin kawar da batagari daga cikinmu. Haka ne zai kawo zama lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban kasa amma ba daidai ba ne mu rinka dora laifin aukuwar miyagun ayyuka ga wata kabila ita kadai, domin akwai bara-gurbin mutane a cikin kowace kabila ko al’umma. Muna jinjina wa jami’an tsaro da suka fara kama mutanen da ake zargi da kisan matar. Sai dai muna fata za su ci gaba da binciken kwakwaf domin gano ainihin wadanda ake zargi,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Shi kuwa Alhaji Muhammadu Nasamu Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Jihar Ekiti cewa ya yi, “Turo Mataimakin Shugaban Kasa don ganawa da manyan Sarakunan Yarbawa da Shugaba Buhari ya yi, abu ne mai kyau da zai murkushe barazanar wargaza kasar nan da wadansu tsirarrun mutane suke yi domin cimma buri na kashin kansu. Ina so ku sani cewa, akwai ’yan ta’adda masu fakewa da Fulani domin bata sunan Shugaba Buhari da Fulani baki daya. Ina  kira ga mahukunta da ’yan Najeriya su nemo mafita ta hanyar zama tare bisa teburin shawara a yi gyara a wurin da ya lalace kuma a yi hakuri tare da yafe wa juna domin rabuwar kasa babu alheri ko kadan a ciki. Kuma ina kira ga Dattawan Arewa su janye batun da suka yi wanda ya haifar da ka-ce-na-ce a tsakanin jama’arsu domin samun zama lafiya.”

A zantawa da Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na Jihar Ondo, Alhaji Bello Garba, ya fara ne da rokon Allah Ya yi wa Shugaba Buhari jagoranci kan irin wannan muhimmin mataki da yake dauka domin hada kan Najeriya. Ya ce, “Muna zaune a cikin wannan jiha ta Ondo inda wadansu mutane da ba a san ko su wane ne suka  harbe wannan mata. Abin da muke cewa shi ne a tabbatar da yin bincike tsakani da Allah domin gano ko wane ne ya aikata wannan danyen aiki, amma ba yada jita-jitar da za su janyo raba kasa ba. Ya kamata al’ummar Yarbawa da Ibo da suke zaune a Arewa su fito su bayyana irin zaman jin dadi da suke yi a Arewa ba tare da takura ba. Ina ganin idan suna yin haka a lokuta daban-daban zai sa shugabanninsu a Kudu da ke yada jita-jita da neman raba kasa za su gane kuskurensu da ka iya haifar da mummunar illa ga Najeriya idan suka ci gaba da yin haka,” inji shi.