✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun gano dabarun dakile amfani da katin zabe na bogi – INEC

Kwamishinan Hukumar Zabe ta Kasa da ke Jihar Nasarawa, Malam Abdulrahman Uthman ya ce a shirye-shiryen da hukumar ke yi kan zabubbukan 2019, tuni ta…

Kwamishinan Hukumar Zabe ta Kasa da ke Jihar Nasarawa, Malam Abdulrahman Uthman ya ce a shirye-shiryen da hukumar ke yi kan zabubbukan 2019, tuni ta inganta na’urorinta na tantance katin zabe don tabbatar da ba a yi amfani da katin zabe na bogi a lokutan zaben ba.

Kwamishinan ya sanar da haka ne a jawabinsa a wajen wani taron zaman lafiya a kan hanyoyin magance rigingimun siyasa kafin da bayan zabubbukan 2019 a jihar, wanda Hukumar Tsaro ta Cibil Defence a jihar ta shirya a Lafiya a karshen makon jiya.

Ya ce “Muna tabbatar wa duniya baki daya cewa za mu gudanar da ayyukanmu na shiryawa da gudanar da ingantattun zabubbuka a shekarar 2019 ba tare da an samu matsala ba. Kuma za mu bayyana duk wanda ya yi nasara ko daga wace jam’iyya ce ba tare da nuna bambanci ba.

“A kan haka ne ma ya sa tuni muka inganta wadannan na’urorin namu na tantance katin zabe wadanda za mu yi amfani da su a lokutan zaben don gano katunan zabe na bogi da wasu ke yin amfani da su a lokutan zabe a jihar da kasa baki daya. Ba shakka dubun ire-iren wadannan masu yin amfani da katunan zabe na bogi za ta cika a wannan karo sakamakon wannan muhimmin mataki da muka dauka. Domin a bana mun sarrafa na’urorin ne ta yadda da zarar aka sanya katin zabe na bogi a cikinsu, za su tantance su gano cewa jabu ne,” inji shi.

Kwmishinan ya nuna takaicinsa game da yadda wadansu ’yan siyasa a jihar da kasa baki daya masu son kansu ke yin amfani da matasa a lokutan zabe wajen ta-da-zaune- tsaye, inda ya shawarci matasa su guji barin irin wadannan ’yan siyasa suna amfani da su wajen ta da hargitsi, a cewarsa hukumar zabe za ta hada hannu da jami’an tsaro wajen gano tare da hukunta duk wanda aka kama da laifin a lokutan zaben.

Ya gargade su dangane da tare hanyoyi don hana masu zabe kada kuri’unsu da kwace akwatunan zabe da sauransu, inda ya ce a karon nan hukumar za ta tabbatar doka ta yi aiki a kan duk wanda aka kama da laifi.

A jawabin Kwamandan Hukumar Cibil Defence a jihar, Malam Muhammed Fari ya tabbatar wa mahalarta taron cewa dukan hukumomin tsaro a jihar sun amince su yi aiki tare da Hukumar INEC don tabbatar an gudanar da zabubbukan cikin kwanciyar hankali ba tare da an samu matsala ba. Ya ce hukumomin tsaron sun kammala dukan shirye-shirye musamman horar da jami’ansu a kan dabarun hanawa ko magance rigingimu da ka iya aukuwa kafin da lokaci da bayan zabubbukan na 2019 da ke tafe.

Ya ce saboda haka hukumar ta ga dacewar shirya taron don neman hadin kan ’yan siyasa da al’ummar jihar daga fannonin rayuwa daban-daban don cimma wannan buri. Daga nan sai ya bukaci mahalarta taron su tabbatar sun bai wa dukan hukumomin tsaro a jihar cikakken goyon baya a wannan bangare don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu kafin da lokaci da kuma bayan zabubbukan.

Wadansu daga cikin mahalarta taron da suka yi jawabi sun bukaci al’ummar jihar su hada kai don cimma wannan buri, inda suka yi fatar alheri a lokutan zaben.

Jihar Nasarawa dai tana daga cikin jihohin kasar nan da ake yawan fuskantar tashin-tashina da yin amfani da katunan zabe na bogi da sauransu a lokutan zabubbukan siyasa.