Da Dumi Dumi

Mun kafa Kungiyar All Women Inclusive ce don kwato hakkokin mata – Balkisu Abdullahi

Shugabar Kungiyar All Women Inclusive,  Hajiya Balkisu Abdullahi, ta ce sun kafa kungiyar ce don taimaka wa mata da kuma kwato musu hakkokinsu.

Shugabar ta fada wa Aminiya cewa kungiyar tana yaki ne da yi wa kananan yara mata fyade da gyara zamantakewar aure da kuma kwato wa mata hakkinsu, sannan ta tallafa wa marasa galihu musamman masu nakasa. Ta ce suna koya musu sana’o’in hannu da b asu jari idan suka koyi sana’ar don dogara da kansu.

A cewarta, yanzu haka kungiyar tasu ta shiga tsakani don kwatowa wadansu mata sama da 4,000 hakkinsu da wata  mai suna Jamila Garba Gambo ake zargin ta damfare su sama da Naira miliyan 40 da sunan tallafi.

Ta ce Jamila ’yar Jihar Bauchi ce, amma ta zo Gombe inda ake zargin ta damfari matan da sunan cewa wata kungiya daga kasar Saudiyya ta kawo wani tallafi ga matan Najeriya marasa karfi da suke son aurar da ’ya’yansu ko zuwa Umara ba su da karfi ta hanyar yin rajista da ita a kan Naira 15,000.

“Ganin ita Jamila ta dauki lauya kuma mu kungiyarmu ta kwato wa mata hakki ne, ya sa aka nemi mu shiga lamarin, mun shiga mun sa a tsare ta don a samu sauki; saboda mata sun taso kuma abin zai vaci. Da aka tsare ta kwana biyu aka sa alkalin ya sake ta ba tare da ta biya ba, shi ne mu kuma muka shigar da koke ga Hukumar EFCC,” inji Balkisu.

ADVERTISEMENT

Ta kara da cewa daga kafa kungiyar zuwa yanzu sun sasanta rikice-rikicen ma’aurata da wadanda ake yi wa auren dole da yawa.

Balkisu ta ce sun shigar da korafe-korafe shida a gaban wasu kotuna a jihar kan yi wa kananan yara ciki da sasanta auren dole da makamantansu inda aka samu maslaha.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya