✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kafa Kungiyar Zamfara Solidarity domin ciyar da al’ummarta gaba  – Aminu Riyo

Zamfarawa mazauna  yankin Kudu maso Kudu sun kafa Kungiyar Zamfara Solidarity Association don nuna goyon bayansu ga Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle sakamakon nasarar…

Zamfarawa mazauna  yankin Kudu maso Kudu sun kafa Kungiyar Zamfara Solidarity Association don nuna goyon bayansu ga Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle sakamakon nasarar da ya samu  cikin kankanen lokaci inda ya fara dawo da martabar jihar bayan karbar ragamar mulkin jihar.

Da yake yi wa wakilin Aminiya karin haske game da dalilansu na kafa kungiyar, Shugaban Kungiyar a Jihar Kuro Riba Alhaji Aminu Bello Muhammad wanda kafi sani da Aminu Riyo ya ce “Abin da ya jawo hankalinmu muka kafa wannan kungiya shi ne mu mazauna Kurmi mun lura cikin kankanen lokaci gwamnatin Matawalle tana samun nasara dawo da martabar Jihar Zamfara wajen samar da zaman lafiya da tsaro kuma tana dawo da martabar jihar a idon duniya. Sannan mu da ke nan Kalaba a Jihar Kuros Riba baya ga mubaya’a ga gwamnatin muna taimakon junanmu wadanda mafi yawancinmu ’yan kasuwa ne, wadanda idan Allah Ya jarabci wani dan uwanmu da wata matsala za mu taimaka masa da karfin aljihunmu bakin gwargwado domin mu ga ya samu waraka ko sauki.”

Ya ce “Haka kuma bayan taimaka wa juna muna yunkurin mu ’yan asalin Jihar mazauna jihohin Kudu maso Kudu mu rika taimaka wa gwamnati da shawarwari da kuma adduo’i.”                                                                                                                                                   Shugaban na Kungiyar Zamfara Solidarity Association ya ce babban kalubalen da suke fuskanta shi ne wadansu daga cikin al’ummar Jihar Zamfara mazauna Kudu  kamar ba su fahimci manufar kafa kungiyar ba “Amma muna nan muna bakin kokari mu ga mun fahimtar da su domin gane manufarmu ta alheri ce da kuma ci gaban jiharmu da duk wani dan asalin Jihar Zamfara mazaunin wajen jihar,” inji shi

.Haka nan kuma Aminu Riyo ya ce za su hada karfi da karfe da kafafen yada labarai na kasar nan domin yayata manufofinsu domin sauran ’yan asalin Jihar Zamfara da ke sauran sassan kasar nan su zo a gudu tare a tsira tare.

A karshe shugaban kungiyar ya yi fatan al’ummar jihar za su ba gwamnatin Bello Matawallen Maradun da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa bisa jajircewarsu wajen dawo da martabar jihar cikin kankanen lokaci musamman a fannin zaman lafiya.