✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kafa kungiyarmu ne don zaman lafiya – Shugabanin ’yan acaba

Shugabannin kungiyar ’yan Acaba da ke unguwar Fagba a jihar Legas sun bayyana cewa sun kafa kungiyarsu ne domin zaman lafiya da hadin kai.Shugaban shirye-shirye…

Shugabannin kungiyar ’yan Acaba da ke unguwar Fagba a jihar Legas sun bayyana cewa sun kafa kungiyarsu ne domin zaman lafiya da hadin kai.
Shugaban shirye-shirye na kungiyar, Umar Adamu ne ya bayyana wa Aminiya hakan a karshen makon da ya gabata cewa kungiyar na dada bunkasa. Ya ce: “Ka sani duk inda aka samu mutane suna sana’a daya to idan suna so su ci gaba sai sun kafa kungiya. Shi ya sa muka kafa wannan kungiya domin mu zauna lafiya kuma mu samu hadin kai. Tun da muka kafa ta muna samun ci gaba da bunkasar tattalin arziki sosai.”
Ya ci gaba da cewa, “Mun samu nasarori da dama wadanda suka hada da raguwar kamen da jami’an tsaro suke yi mana da kuma tauye mana hakki da suke yi, ba gaira ba dalili. Sannan kuma a da a rarrabe muke, amma sakamakon kungiyar nan mun samu hadin kai.”
A nashi bangaren, Mataimakin shugaban kungiyar, Malam Aliyu Muhammed ya bayyana cewa kungiyar ta cimma burin da aka kafa ta dominsu.
Sai dai ya ce  har yanzu wasu ’yan sanda suna kama mambobin su, suna karbar kudi a wurinsu.Ya kara da cewa suna daukar matakai domin kawo karshen kame-kamen da ’yan sanda suke yi wa mambobinsu.
Jami’in da yake sanya ido a kan ’yan kungiyar, Abubakar Idris ya bayyana cewa matsalar da ke damun sa ita ce halin-ko-in-kula na mambobin kungiyar.
“Shi ya sa idan muka fahimci wasu daga cikin mambinmu ba sa ayyukan da suka kamata, sai mu canja su saboda shi aiki sanya ido a kan mambobin kungiyar aiki ne mai wahalar gaske, sai an samu jajirtattu sannan za a cimma burin da aka sanya a gaba,” inji shi.